Rikici Ya Kaure: Amarya Ta Farmaki Ango da Naushi a Ranar Daurin Aure, Bidiyon Ya Yadu

Rikici Ya Kaure: Amarya Ta Farmaki Ango da Naushi a Ranar Daurin Aure, Bidiyon Ya Yadu

  • Bidiyon wani bikin aure da aka yi a Rwanda ya nuno amarya da ango suna tafiya hannunsu cikin juna kafin dirama ya kaure
  • Kwatsam matar ta kunsawa mutumin naushin bazata yayin da jama'ar da ke wajen suka gaggauta shiga tsakani
  • Wasu masu amfani da soshiyal midiya sun nuna takaicinsu kan lamarin yayin da wasu ke mamakin ko dai shiri ne

Rigima ya kaure a wajen wani bikin aure bayan amarya ta farfmaki ango a wajen shagalin biki a Rwanda.

Fada ya kaure a wajen biki
Rikici Ya Kaure: Amarya Ta Farmaki Ango da Naushi a Ranar Daurin Aure, Bidiyon Ya Yadu Hoto: Actionz TV.
Asali: UGC

An sha dirama a wajen shagalin bikin aure a Rwanda

Bidiyo shagalin bikin ya nuno amarya da ango suna fita daga wani katafaren gini kafin tunkarar coci don daurin aurensu.

Angon ya sanya kwat da wando yayin da amaryar ta sanya farar doguwar riga irin na amare. Kawayen amarya da abokan ango sun jeru sanye da anko iri guda.

Kara karanta wannan

Babu Ruwanmu da NEPA: Budurwa Ta Nunawa Duniya Katafaren Gidan Iyayenta a Bidiyo, Jama'a Sun Shiga Mamaki

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Komai na ta tafiya daidai har sai da amarya ta tubure.

Masoyan sun rike hannu yayin da amaryar ke rike da fure. Kwatsam sai ta saki hannun angon sannan ta kwashe shi da mari ta keya.

Sai ta jefar da furen sannan ta tattara rigarta ta yi shirin fada, kafin aminin ango ya yi gaggawan shiga tsakani.

Aminin angon da sauran kawayen amaryar sun yi tsalle don rirriketa, yayin da take kokarin sake farmakar angon nata.

Sun sha fama a kokarinsu na lallashin matar wacce aka kwantar a kasa. An gano wasu daga cikin kawayen amaryar suna kuka.

Daga bisani, an gano amaryar tana magana da wata mata a kan wayar tarho cikin harshen Kinyarwanda.

Jama'a sun yi martani

Shallot Ruth:

"Bakin ciki ya dabaibaye ni. Na kasa rike hawayena."

Kara karanta wannan

Ana Tsaka Da Shagalin Biki An Fasawa Amarya Ido a Jihar Kano, yace ba zai yarda ba

Annet Queen: '

"Wannan gaskiya ne ko dai shirin fim."

Dativa Joachim:

"Shirin fim ne."

Nzigiyabagabo Theoneste:

"A kodayaushe aure na fuskantar makiya da dama."

CM:

"Wannan talla ne."

Kalli bidiyon a kasa:

A Soshiyal midiya muka hadu kuma na yi wuff da abina, Matashiya da ta auri bature

A wani labarin, wata matashiya da ta shafe shekaru hudu da auren baturen mijinta ta magantu a kan soyayyarsu.

Yayin da take murnar cikarsu shekaru hudu da aure, matashiyar ta ce a dandalin kulla soyayya suka hadu har ta kai su ga aure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel