Muna da Katangar Lantarki, Ga Solar Babu Ruwanmu da NEPA: Budurwa Ta Nuna Katafaren Gidan Iyayenta a Bidiyo

Muna da Katangar Lantarki, Ga Solar Babu Ruwanmu da NEPA: Budurwa Ta Nuna Katafaren Gidan Iyayenta a Bidiyo

  • Wata budurwa ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta nuna katafaren gidansu mai kofofin da harbin bindiga baya shiga
  • Da na’urar rimut ake bude babban kofar shiga gidan kuma akwai katangar lantarki saboda tsaro da wutan solar
  • Mutane da dama da suka so raina mata hankali a kan arzikin gidansu sun samu amsa daidai da su

Wata matashiya yar Najeriya @_goldia, ta ja hankalin mutane da dama da wani bidiyo da ta wallafa a TikTok inda ta haska katafaren gidansu.

A bidiyon, budurwar ta bayyana cewa gidansu na da kofofi da harbin bindiga baya iya shiga da katangar lantarki.

Budurwa da gida
Muna da Katangar Lantarki, Ga Solar Babu Ruwanmu da NEPA: Budurwa Ta Nuna Katafaren Gidan Iyayenta a Bidiyo Hoto: TikTok/@_goldia
Asali: UGC

Da take hasko cikin gidan, ta bayyana cewa suna da na’urar yin kankara. Akwai kuma wajen shakatawa a ciki.

Masu amfani da TikTok da dama sun sha mamaki ganin cewa gidan budurwar na dauke da abubuwan da a mafarki kawai suke ganin.

Kara karanta wannan

Ana Tsaka Da Shagalin Biki An Fasawa Amarya Ido a Jihar Kano, yace ba zai yarda ba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun yi al’ajabin irin tarin dukiyar da Allah ya yiwa wannan iyali nata.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama’a a kasa:

Holy Grant ta tambaya:

“Shin wadannan abubuwan sabon abu ne?"

Ta amsa:

“Eh ba sabon abu bane saboda kowa na da kofofi da harbin bindiga baya shiga da wutan solar.”

Abiodun Ibitoye ya ce:

“Na zata wannan ba sabon abu bane, amma bari nayi shiru kafin wani ya caccake ni.”

Oyewumi Mueez Bolaji ya ce:

“Ku masu ihun ba sabon abu bane. Ku kuka san inda kuke ganin ba komai bane ni da ku mun san cewa wannan shine abun da ake kira da arziki don haka ku daina bakin ciki.”

Umutesi Celine ta ce:

“Fada mun kina da kudi ba tare da kin fada mun kina da kudi ba.”

Kara karanta wannan

Jerin Matsaloli Jingim da ke Jiran Duk Wanda Zai Gaji Shugaba Buhari a Aso Rock

Gracie ta ce:

“Sai yau ne wannan talaucin ya yi mun ciwo.”

Matashiya ta fashe da kuka bayan ta sauka daga jirgin sama

A wani labarin kuma, wata matashiya yar Najeriya ta fashe da kuka tare da godiya ga Allah bayan ta sauka daga jirgin sama.

Matar ta yi birgima a kasa tana mai godiya ga Ubangijinta lamarin da yasa mutane tunanin ko dai karo na farko da takd shiga jirgi kenan a rayuwarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel