Mun Hadu a Dandalin Sadarwa: Matashiya Ta Baje Kolin Baturen Mijinta da Suka Hadu a Soshiyal Midiya

Mun Hadu a Dandalin Sadarwa: Matashiya Ta Baje Kolin Baturen Mijinta da Suka Hadu a Soshiyal Midiya

  • Wata matashiya ta garzaya shafin soshiyal midiya don murnar cika shekaru hudu da auren sahibinta wanda Bature ne
  • Da take bayyana cewa sun hadu ne a wani dandalin kulla soyayya, budurwar ta kara da cewar sun tashi daga abokai zuwa abokan rayuwa
  • Mutane da dama da suka yi martani ga bidiyon soyayyar sun bukaci matar da ta fada masu sunan dandalin soyayyar

Wata matashiyar budurwa ta wallafa wani bidiyo don murnar cika shekaru hudu da aurenta da baturen mijinta, inda ta bayyana yadda abun ya fara.

Matashiyar ta bayyana cewa shekaru hudu da suka gabata, sun hadu a dandalin kulla soyayya. Yayin da suke matsayin saurayi da budurwa, masoyan na yawan yin kira ta bidiyo.

Ma'aurata
Mun Hadu a Dandalin Sadarwa: Matashiya Ta Baje Kolin Baturen Mijinta da Suka Hadu a Soshiyal Midiya Hoto: TikTok/@vibeswithbeccaa
Asali: UGC

Labarin soyayya mai dadi

Hotuna da suka bayyana yan sakanni da fara bidiyon ya nuna cewa ma’auratan sun bunkasa soyayyarsu inda suka hadu ido da ido.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya Sun Zagaye Mai Kama Da Shugaba Buhari a Wani Bidiyo Da Ya Yadu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Harma sun yi yar kwarya-kwaryar liyafa tare. Daga bisani sai masoyan suka yi aure kuma tun lokacin suke tare inda a yanzu suka shekara hudu.

Kyawawan hotunan da ma’auratan suka dauka tare cikin shekarun ya sa mutane da dama sun jinjina masu. Aurensu ya yi albarka da ‘da daya.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

scorpioismysign ta tambaya:

“A wani dandalin soyayar ku ka hadu don Ina neman masoyi na gaskiya nima?

SHADRACK ya ce:

“Diyar wani ta gano ni dan Allah.”

dellykorkor ta ce:

“Allah ya yi mun irin taki nima.”

callmenanaaba ta ce:

“Na taya ku murna Ina fatan samun nawa masoyin Kamar yadda ku ka samu.”

Efya_conny ta ce:

“Allah ya yi mun irin taki Amin.”

Mariam Audu ta ce:

“A wannan dandalin soyayyar za mu kwana yau dole mu cimma irin haka a 2023 dinnan.”

Kara karanta wannan

Ina Biyan Kudin Haya N800k Duk Shekara: Budurwa Ta Nuna Cikin Dakinta Da ke Da Wuta 24/7

the.real_zelda ta tambaya:

“Wani dandali dan Allah don na bude shafi?”

abenaodo116 ta ce:

“Na taya ki murna yar’uwa...ki tayani samun daya na gaji da zama haka ba mashinshini.”

A wani labarin kuma, wata matashiyar budurwa ta saki bidiyon irin sauyawar da ta yi cikin watanni uku da komawarta Turai da zama.

Matashiyar wacce ta fito daga kasar Ghana ta ce duk wanda ya ce Turai bai yi ba karya yake yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel