Zaben Bana Na Tinubu Ne, Lokacin da Zai Ci Rabonsa Ya Yi, DG Na APC Ga ’Yan Najeriya

Zaben Bana Na Tinubu Ne, Lokacin da Zai Ci Rabonsa Ya Yi, DG Na APC Ga ’Yan Najeriya

  • Dino Melaye ya yada wani bidiyon gangamin kamfen APC, inda ake fadawa ‘yan Najeriya yanzu lokaci ne ga Tinubu ya gaji Buhari
  • Maganar dai na fitowa ne daga bakin daraktan kamfen APC na kasa, gwamna Simon Lalong na jihar Filato yayin gangami a birnin Ilorin a jihar Kwara
  • Lalong ya ce lokacin da Tinubu ke gwamna a Legas, bai da son kai da kwadayi, don haka yanzu lokacinsa ne ya more kujerar shugaban kasa

Kakakin kamfen shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Sanata Dino Melaye ya yada wani bidiyon dake nuna lokacin da ake tallata Tinubu gabain zaben 2023.

Bidiyon da aka yada a Twitter ya nuna tawagar kamfen Tinubu lokacin da take kafen a birnin Ilorin ta jihar Kwara.

A bidiyon, daraktan gangamin kamfen na APC, gwamna Simon Lalong ya ce, yanzu lokaci ne ga Tinubu ya zama shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Wike Ya Samu Tangarɗa, Gwamnan G-5 Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Kan Yuwuwar Haɗewa da Atiku

Lokacin Tinubu ya ci rabonsa
Zaben Bana Na Tinubu Ne, Lokacin da Zai Ci Rabonsa Ya Yi, DG Na APC Ga ’Yan Najeriya | Hoto: Dino Melaye, Joe Igbokwe
Asali: UGC

Tinubu bai da son kai

Gwamnan na jihar Filato ya ce Tinubu ba mutum ne mai son kai ba, inda yace kowa ya ga hakan a lokacin da yake gwamna a jihar Legas.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar Lalong, yanzu lokaci ya yi da ya kamata a marawa Tinubu baya domin yi masa sakayya ga ayyukan da ya yi na karimci a Legas.

Lalong ya fada a cikin bidiyon cewa:

“Emilokan, Asiwaju ya yi aikin kirki, yanzu lokacinsa ne, lokacinsa ne, lokacinsa ne.
“Idan ka ci kai kadai kai kadai za ka mutu. Bai ci shi kadai ba. To wannan karon lokacinsa ne ya ci. Wannan yasa Emilokan ke da matukar muhimmanci.”

Ina hujjoji a kas,a Tinubu dan ta’adda ne, inji Dino Melaye

A wani labarin kuma, jigon PDP Dino Melaye ya bayyana cewa, yana da hujjoji a kasa da ke nuna ta’addanci Bola Ahmad Tinubu.

Kara karanta wannan

Dino Malaye Yace Ta Karewa Tinubu A Yankinsa Na Kudu Maso Yamma, Tunda Shugabannin Yankin Basa Yinsa

Melaye na martani ne ga batutuwa da APC ta taso dasu game da Atiku tare da kai maganar gaban kotu cewa ana zarginsa da rashawa da cin kudin kasa.

APC ta maka Atiku da PDP a kotu kan cewa, ya kamata a hana Atiku takara saboda wasu ayyukan rashawa da taba aikatawa a baya. Ba wannan ne karon farko da maganganu irin wadannan ke fita ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel