An Samu Matsala a G5, Na Kusa da Wike Ya Yi Magana Kan Sasantawa da Atiku

An Samu Matsala a G5, Na Kusa da Wike Ya Yi Magana Kan Sasantawa da Atiku

  • Gwamna Samuel Ortom na Benuwai, babban na kusa da Wike ya yi bayanin yuwuwar sasantawa da Atiku Abubakar
  • Ortom yace APC ba ta da wata kofar lashe ko zabe ɗaya a jihar Benuwai, bisa haka ya bukaci shugabannin PDP su duba bukatar G5
  • Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a wurin taron karban mambobin APC da suka sauya sheka a mazabar Ministan Buhari

Benue - Ga dukkan alamu an samu tangarɗa a tawagar fustattun gwamnonin jam'iyar PDP duk da tsawon lokacin da suka shafe suna gina tawaga mai karfi.

Gwamnonin karakashin sunan da ake kiransu 'gwamnonin G-5 ko tawagar masu gaskiya' sun sha alwashin ba zasu tallata dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar, ba har sai Iyorchia Ayu ya yi murabus.

Atiku da gwamnonin G5.
An Samu Matsala a G5, Na Kusa da Wike Ya Yi Magana Kan Sasantawa da Atiku Hoto: Atiku Abubakar, Samuel Ortom, Nyesom Wike
Asali: Twitter

Shin gwamnonin G-5 sun shirya da bangaren Atiku?

Kara karanta wannan

2023: Ana Gan da Zabe, Bola Tinubu Ya Gamu da Babbar Matsala a Jihar Shugaba Buhari

Gwamnonin G-5 sun kunshi Seyi Makinde na jihar Oyo, Samuel Ortom na jihar Benuwai, Okezie Ikpeazu, na jihar Abiya, Nyesom Wike na Ribas da Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun bukaci shugaban PDP na kasa ya yi murabus a zakulo ɗan kudancin Najeriya ya maye gurbinsa da nufin yin adalci da daidaito tunda tikitin shugaban kasa ya tafi Arewa.

Amma ga dukkan alamu, wasu daga cikin gwamnonin sun fara janye wa daga wannan bukata a daidai lokacin da harkokin kamfe suka kankama gabanin watan Fabrairu.

Ortom, wanda ake kallon ya fi kusa da jagoran G-5 watau Wike, ya bayyana kwarin guiwar cewa Atiku da shugabannin PDP zasu warware batun dake gabansu cikin lokacin domin zaman lafiya ya dawo.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a wurin kamfen PDP a karamar hukumar Turka sa'ilin da yake karban masu sauya sheka daga APC na mazabar jagoransu, George Akume.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban PDP, Dan Majalisa da Wasu Kusoshi Sun Bar Tafiyar Atiku, Sun Koma Kwankwaso

A cewar Ortom, APC ba ta da damar lashe zaben kujera ɗaya a watan Fabrairu da Maris, don haka ya roki shugabannin PDP su gaggauta magance fushin G-5.

Kar ku zabe mijina a karo na 2 idan ya gaza - Matar Tinubu

A wani labarin kuma Matar dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, ta shawarci yan Najeriya game da babban zaben 2027

Sanata Oluremi Tinubu tace mijinta abokin gaminsa Shettima zasu gayara Najeriƴa amma idan suka gaza bayan shekara hudu a guje su.

Matar Tinubu ta yi wannan furuci ne a Ralin mata na tallata Tinubu/Shettima a shiyyar kudu maso gabas wanda ya gudana a Owerri, babban birnin jihar Imo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel