Dalilin Da Yasa Har Yanzu Bamu Bayyana Wanda Muke Goyon Baya Ba: Dattawan Arewa

Dalilin Da Yasa Har Yanzu Bamu Bayyana Wanda Muke Goyon Baya Ba: Dattawan Arewa

  • Sauran kwanaki 37 zaben shugaban kasa Najeriya da zai gaji Shugaba Muhammadu Buhari
  • Kungiyoyin ra'ayi da dattawa a Njeriya daban-daban sun bayyana wanda suke goyon baya
  • Har yanzu ba'a ji daga bakin kungiyar dattawa Arewa 'Northern Elders Forum' ba

Abuja - Kungiyar dattawan Arewa ta bayyana dalilan da ya sa har yanzu bata bayyana zabinta cikin yan takarar kujerar shugaban kasa a zaben da zai gudana watan gobe ba.

Za'a gudanar da zaben shugaban kasan Najeriya ranar 25 ga Febrairu, 2023.

Wadanda ake yiwa kallon cikinsu daya zai lashe zaben shugaban kasan sun hada Peter Obi (Labour Party), Bola Tinubu (All Progressives Congress) , Atiku Abubakar (Peoples Democratic Party) da Rabiu Kwankwaso (New Nigeria Peoples Party).

Kakakin kungiyar dattawan Arewa, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce ba zasu yi gaggawan ayyana wanda zasu goyi baya ba duk da ana sauran yan makonni zabe.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Manyan Kura-Kurai Aka Tafka, Rashin Shugabanci Na Kwarai a Kasar Nan na Shekaru 24 ne ya Tsundumata Halin da Muke Ciki

Ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa a shirin Focus Nigeria na tashar AIT.

BAba Hamed
Dalilin Da Yasa Har Yanzu Bamu Bayyana Wanda Muke Goyon Baya Ba: Dattawan Arewa Hoto: ChannelsTV
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Su wa kungiyar ta goyi baya a baya

A shekarar 2015, dattawan arewan sun goyi bayan Shugaba Muhammadu Buhari amma a 2019 suka juya masa baya suka goyi bayan Alhaji Atiku Abubakar.

Hakeem Baba-Ahmed yace:

"Wannan karon muna takatsantsan - bamu son yin gaggawan hukunci. Akwai saura makonni shida kan mu yanke shawara. Muna bibiyan abubuwan da yan takara ke yi, abubuwan da suka fadi, har da yan takaran gwamna da majalisa."

Ya kara da cewa zasu sanar da wanda suke goyon baya kafin ranar zabe saboda ba zasu bari Arewa ta zauna ba tada matsaya ba, rahoton PremiumTimes.

Ya ce Najeriya ba ta bukatan shugaban kasa da zai nuna bangarancin kabila ko addini kuma wanda zai iya yanke shawari ko da mutane ba zasu ji dadi ba.

Kara karanta wannan

Ba Wanda Zai Ci Bulus: Atiku Ya Gindaya Sharadin Baiwa Mambobi da Manyan PDP Mukami Idan Ya Ci Zabe

Irin 'Yan Siyasar da Mutane Za Su ba Kuri’arsu a Zaben 2023 - Fastocin Kudu

A wani labarin, fastocin cocin katolika na yankin kabilar yarabawa (kudu maso yammacin Najeriya) sun yi kira ga al'ummarsu da su zabi shugabanni na gari a zabe mai zuwa.

Wannan ya bayyana ne a takardar da shugaban kungiyar limaman, Rabaren Gabriel Abegunrin da sakatarensa, Rabaren John Oyejola suka fitar bayan wani taro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel