CBN Ya Tabbatar da Emefiele Ya Zo Aiki, ’Yan Sanda Sun Musanta Cewa Sun Mamaye Gidansa

CBN Ya Tabbatar da Emefiele Ya Zo Aiki, ’Yan Sanda Sun Musanta Cewa Sun Mamaye Gidansa

  • Rundunar 'yan sandan Najeriya ta karyata labarin cewa, jami'anta sun mamaye gidan gwamnan CBN
  • Hakazalika, babban bankin ya ce gwamnan CBN Godwin Emefiele ya fito aiki kamar yadda ya saba ba tare da matsala ba
  • Majiya ta ce, jami'an tsaro sun mamaye gidan gwamnan CBN bisa zargin zai iya guduwa daga kamun da ake son yi masa

FCT, Abuja - An ruwaito cewa, gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Mr. Godwin Emefiele ya zo aiki kuma yana ci gaba da harkokinsa, a cewar bankin.

Wannan batu na fitowa ne daga CBN bayan da rahotanni a jiya Talata 17 ga watan Janairu suka bayyana cewa, an ga jami’an ‘yan sanda sun mamaye gidan gwamnan da ke Maitama, Abuja da dare.

Gwamnan CBN ya fito aiki, inji babban banki
CBN Ya Tabbatar da Emefiele Ya Zo Aiki, ’Yan Sanda Sun Musanta Cewa Sun Mamaye Gidansa | Hoto: dailypost.com
Asali: UGC

Mai magana da yawun babban bankin, Mr. Osita Nwanisobi ya tabbatarwa Channels Tv cewa, a ranar Laraba da Safe an ga Emefiele, wanda ya dawo bakin aiki tun ranar Litinin bayan kwashe kwanaki yana hutun aiki.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Gwamnonin Jihohi 36 Za Su Titsiye Gwamnan Babban Bankin CBN

‘Yan sanda sun magantu

A bangare gudam rundunar ‘yan sanda ta karyata cewa jami’anta sun mamaye gidan Mr. Emefiele a jiya Talata.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kakakin rundunar ‘yan snadan, Muyiwa Adejobi ya bayyana cewa, rahotannin da ke cewa ‘an tura jami’ai gidan gwamnan ba gaskiya bane kuma bai san da hakan ba.

Ya zuwa safiyar Laraba 18 ga watan Janairu, Channels Tv ta ce ta ziyarci gidan gwamnan na CBN, amma bata ga alamar wasu sabbin ‘yan sanda da aka kawo face jami’ai biyu da keba da tsaro a gidan.

Ana ci gaba da cece-kuce game da gwamnan babban bankin Najeriya da kuma yiwuwar kama shi bisa zargin cinye wasu makidan kudade na kasa.

DSS ta mamaye ofishin gwamnan CBN

A wani labarin kuma, kunji yadda aka ruwaito cewa, jami'an hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta mamaye ofishin gwamnan CBN a cikin makon nan.

Kara karanta wannan

Karin bayani Gwamnan CBN ya shiga tasku, 'yan sanda sun mamaye gidansa da dare

Wannan na zuwa ne awanni kadan bayan da aka ce gwamnan ya dawo daga hutun da ya tafi zuwa kasar waje a karshen shekara.

Ana zargin gwamnan CBN Godwin Emefiele da yashe asusun gwamnati, ana ci gaba da nemansa a kotu a Najeriya, amma lamarin ya ci tura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel