Hare-Haren da Ake Cewa Boko Haram Na Kaiwa a Najeriya Karya Ne, Buhari Ya Magantu a Waje

Hare-Haren da Ake Cewa Boko Haram Na Kaiwa a Najeriya Karya Ne, Buhari Ya Magantu a Waje

  • Babu wani bangare a Najeriya da ke karkashin ikon ‘yan ta’addan Boko Haram a Najeriya, cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • Buhari ya magana mai daukar hankali yayin da ganawarsa da shugaban Dhabi Peace Forum, Shaykh Abdullah Bn Bayyah a ranar Talata 17 ga watan Janairu
  • A cewar Buhari, gwamnatinsa za ta ci gaba da tabbatar da kakkabe ‘yan ta’adda a dukkan fadin kasar da ke nahiyar Afrika

Nouakchott , Mauritania - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce, a yanzu babu wani bangare a Najeriya da ke karkashin ikon ‘yan ta’addan Boko Haram.

PM News ta ruwaito cewa, shugaba Buhari ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da shugaban zauren zaman lafiya na Abu Dhabi, Shaykh Abdullah Bin Bayyah a ranar Talata 17 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Kwamandoji Abu Ubaidah da Malam Yusuf Tare da Mayaka 40 na Boko Haram Sun Sheka Lahira Bayan Luguden NAF

Sun yi wannan ganawa ce a wani taron zaman lafiya da aka gudanar Nouakchott ta kasar Mauritania, inda Buhari ya ce gwamnatinsa ta kwace ikon Boko Haram a kasar.

Buhari ya ce a yanzu babu Boko Haram a Najeriya
Hare-Haren da Ake Cewa Boko Haram Na Kaiwa a Najeriya Karya Ne, Buhari Ya Magantu a Waje | Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Twitter

Da yake bayanin cewa, labaran hara-haren Boko Haram a Najeriya duk na karya ne, shugaba Buhari ya tabbatar da cewa, masu daukar nauyin ayyukan ta’addanci a kasar suna da nufin raba ta ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

“Boko Haram karya ce. Kun ce ilimin zamani na yammacin duniya haramun ne. Yaudara ce. Duk wanda ke daukar nauyinsu so yake ya raba kasar.
“Dukkan wuraren da suka kwace kafin mu zo mun kwato su, kuma muna ci gaba da sake gina yankunan.”

Shugaban zauren zaman lafiya ya yi martani

A cewar rahoton Punch, Shaykh Bin Bayyah ya yaba da kokarin gwamnatin shugaba Buhari wajen fatattakar ‘yan tada kayar baya a kasar.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike Ya Fadi Wata Addu'a 1 da Yake Yawan Yi Wa Shugaba Buhari a Kullum

Ya ce:

“Kana matukar kokari a wannan fannin, kuma shi muke bukatan yi duk inda abu makamancin haka ya tashi a duniya.
“Kana da gogewa da yawa, a matsayin shugaban soji, kuma a matsayin shugaban dimokradiyya da aka zaba har sau biyu kuma tabbas kokarinka abin yabawa ne a kowacce al’umma. Muna maraba da karbarka.”

Daya daga cikin alkawuran da shugaba Buhari ya yiwa ‘yan Najeriya kafin hawansa mulki a 2015 shine karar da ‘yan ta’addan Boko Haram.

A bangare guda, Buhari ya ce akwai masu amfani da addini wajen yada kiyayya don cimma burin siyasa da na arziki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel