Gwamna Wike Ya Fadi Wata Addu'a 1 da Yake Yawan Yi Wa Shugaba Buhari a Kullum

Gwamna Wike Ya Fadi Wata Addu'a 1 da Yake Yawan Yi Wa Shugaba Buhari a Kullum

  • Nyesom Wike ya yabawa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar tunawa da sojojin Najeriya
  • Gwamnan Jihar Ribas ya ce Shugaban kasar ya cancanci yabo wajen yaki da ‘Yan ta’addan Boko Haram
  • Wike yake cewa ba zai daina yi wa Mai girma Muhammadu Buhari da sauran shugabanni addu'a ba

Rivers - Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya yabawa Shugaba Muhammadu Buhari a kan irin kokarin da ya yi wajen yakar masu tada kafar baya.

The Cable ta rahoto Nyesom Wike a ranar Lahadi yana cewa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kokari a bangaren ganin bayan ‘yan ta’adda.

Gwamnan na jihar Ribas ya yi wannan bayani ne wajen bikin tunawa da sojojin Najeriya da aka yi a karshen makon jiya gidan gwamnati da ke Fatakwal.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Tona Asirin Manyan Yan Takara Biyu, Yace Hatsari Ne Babba a Zabe Su a 2023

Wike yake cewa dakarun sojojin Najeriya su ne a gaba-gaba wajen karya ‘Yan ta’addan Boko da ‘yan bindigan da suka addabi wasu yankunan kasar nan.

Gwamnati za ta bar tarihi a Najeriya

An rahoto Wike ya ce namijin aikin da gwamnati mai-ci tayi, zai taimaka wajen ganin an shirya zabuka na kwarai da za a rika tunawa da shugaban kasar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaba Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter
“Ina jinjinawa Shugaban kasarmu, Janar Muhammadu Buhari, GCFR na tsayawa tsayin-daka da ya yi wajen yakar ‘yan ta’addan Boko Haram da ‘yan ta’addan da suka addabi garuruwa a kasarmu.”
Kawo zaman lafiya a yankunan da ba a zaman lafiya da kuma shirya zaben gaskiya da adalci su ne mafi kyawun tarihin da mutum zai bari a kasarmu.
A matsayinmu na shugabanni, dole burinmu ya zama tsare Najeriya da kalubalen wanzar da adalci da tafiya da kowa.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Fadi Wadanda Zai ba Mukamai da Abin da Zai Yi Kafin Kwana 100 a Aso Rock

Saboda haka ba zan daina yi wa Mai girma shugaban kasa da sauran shugabannin kasarmu addu’ar samun nasara a ayyuka da hidimar da muke yi wa kasarmu ba.

- Nyesom Wike

Jaridar Aminiya ta ce Gwamnan Ribas ya yi kira da cewa a maida hankali a kan walwalar jami’an tsaron Najeriya da iyalinsu, ya ce ya kamata a kula da su.

A dalilin haka ne Gwamna Wike ya bada gudumuwar Naira Miliyan 100 domin a kula da tsofaffin sojojin da ke jihar, yace gwamnatinsa ta dade tana wannan.

IBB da Obasanjo a 2007

Kassim Afegbua ya bada labarin yadda aka yi wani zama tsakanin Olusegun Obasanjo da su Aliyu Gusau, Abdulsalami Abubakar da Atiku Abubakar.

Afegbua ya ce an kawo maganar tazarcen Obasanjo a taron, sai Janar Ibrahim Babangida ya dage cewa shugaban kasar ba zai zarce a kan mulki ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel