Dakarun Soji Sun Halaka Kwamandojin Boko Haram 2 da Wasu Mayaka 40

Dakarun Soji Sun Halaka Kwamandojin Boko Haram 2 da Wasu Mayaka 40

  • Wani sabon rahoto ya bayyana yadda dakarun sojin Najeriya suka sheke wasu shugabannin 'yan ta'adda biyu, Abu Ubaida da Mallam Yusuf Abba a jihar Neja
  • Bincike ya tabbatar da yadda shugaban 'yan ta'addan suka gamu da ajalinsu tare mayakansu kimanin 40 a wani gidan kasa a anguwar Kurebe cikin karamar hukumar Shiroro na jihar
  • Wani binciken sirri ne ya tabbatar da yadda 'yan ta'addan ke boyewa a gidan a duk lokacin da dakarun suka kai musu samame, kuma anan ne suka amfani da taki wajen hada abubawa masu fashewa

Niger - An ruwaito yadda dakarun soji suka halaka biyu daga cikin shugabannin 'yan ta'adda, Abu Ubaida da Mallam Yusuf Abba.

Taswirar Neja
Dakarun Soji Sun Halaka Kwamandojin Boko Haram 2 da Wasu Mayaka 40. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

An shekesu ne tare da kimanin mayakansu 40 a wani kangon gida a Kurebe, wata anguwa da tayi fice cikin karamar hukumar Shiroro dake jihar Neja.

Kara karanta wannan

Jami'an NSCDC Sun Damke Mai POS da 'Yan Bindiga Suka Girke Yana Musu Hada-hadar Kudi

A wani rahoto da wakilin Punch ya gani ranar Litinin ya bayyana yadda Abu Ubaida da Abba suka hadu da ajalinsu yayin wata luguden wutar da sojin saman Najeriya (NAF) ta shirya tare da hadin guiwar Operation Whirl Punch, inda ta kai musu samame cikin kwanakin nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda rahoton ya bayyana:

”Idan za a tuna a ranar 22 ga watan Disamba 2022, jirgin yakin NAF ya kai samame ga taron 'yan ta'adda a Kurebe cikin karamar hukumar Shiroro.
"'Yan ta'adda da dama sun rasa rayukansu, amma bai tabbatar idan akwai daya daga cikin shugabannin 'yan ta'adda a harin ba.
"Sai dai, bayan wannan harin, bincike ta kafafe da dama ya bayyana yadda 'yan ta'addan ke boyewa a wani gidan kasan duk lokacin da NAF ta kai samame a yankin.
"Haka zalika, an gano yadda 'yan ta'addan ke boyewa a wannan wurin, inda aka gansu kan babura a karo daban-daban suna dauke da buhunhunan taki zuwa gidan.

Kara karanta wannan

2023: Dubbannin 'Yan SPW Sun Yanke Shawara, Sun Fadi Wanda Zasu Goyi Baya Tsakanin Tinubu da Atiku

"Da wannan takin ne 'yan ta'addan ke amfani wajen hada abubawa masu fashewa.
"Kamar yadda NAF ta bayyana, jiragen yakin sun yI dirar mikiya ne don tabbatar sun tarwatsa gidan da sheke 'yan ta'addan,"

Kakakin NAF, Air Commondore Wap Maigida, ya tabbatar da nasarar luguden wutar jiragen saman.

Katsina: ‘Yan Bindiga sun sace masu bauta 25 daga Coci

A wani labari na daban, wasu miyagun ‘yan bindiga sun yi garkuwa da masu bauta 25 a wata coci da ke Jan Tsauni, karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina.

Har a halin yanzu dai ba su sako ba duk da jami’an tsaro na iyakar kokarin ganin sun ceto su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel