Nasara Daga Allah: Bama-Bamai Sun Sheke Daruruwan Yan Bindiga a Sakkwato

Nasara Daga Allah: Bama-Bamai Sun Sheke Daruruwan Yan Bindiga a Sakkwato

  • Mamba mai wakiltar mazabar Rabah a majalisar dokokin jihar Sakkwato ya yaba da namijin kokarin sojin Najeriya
  • Yace ruwan bama-bama jirgin yakin sojojin ya yi ajalin daruruwan yan bindiga da suka addabi mutanen mazabarsa
  • Tsawon shekaru karamar hukkumar Rabah na fama da ta'addancin ya fashin jeji ba tare an taka masu birki ba

Sokoto - Jirgin yakin rundunar sojin Najeriya ya halaka tulin yan bindigan jeji a kauyen Rarah dake karamar hukumar Rabah ta jihar Sakkwato.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa karamar hukumar Rabah da ke a gabashin yankin jihar Sakkwato tana fama da hare-haren ta'addanci tsawon shekaru.

Jirgin sojin saman Najeriya.
Nasara Daga Allah: Bama-Bamai Sun Sheke Daruruwan Yan Bindiga a Sakkwato Hoto: NAF
Asali: UGC

Yankin karamar hukumar ya haɗa iyaka da karamar hukumar Bakura a jihar Sakkawato da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Mamba mai wakiltar mazabar Rabah a majalisar dokokin jihar, Abdullahi Zakari, yace Sojoji sun yi luguden bama-bamai a mafaka uku, sun sheke daruruwan yan bindiga.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Tono Asalin Matsala, Ya Fadi Abu Ɗaya Tak Da Ya Kawo Yan Bindiga Arewacin Najeirya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan bindiga sun kai hari kauyuka 17

Ɗan majalisar ya bayyana cewa 'yan fashin dajin sun dawo ne daga kai harin ta'addanci lokacin da ruwan bama-bama sojoji ya tura su barzahu.

"Sun kai farmaki kusan kauyuka 17, sun kashe bayin Allah uku sannan suka tattara Shanu suka yi awon gaba da su," inji shi.

Honorabul Zakari ya bayyana wannan aikin na Sojoji da gagarumar nasara lamba daya da aka samu a 'ƴan kwanakin nan.

"Yadda (Sojoji) suka yi hanzarin kawo dauki daga kiran gaggawar da muka masu, suka aiko da jirgin yakinsu abun a yaba ne. Muna fatan su ci gaba da haka saboda 'yan bindiga sun addabi mutanen mu ba tare da an taka musu birki ba."

Bincike ya nuna cewa yan bindigan sun kai hari wasu kauyuka a Kware da Rabah kafin ba zato ba tsammanin su ji ruwan bama-bamai ta ko ina a kauyen Rarah.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Manyan Kura-Kurai Aka Tafka, Rashin Shugabanci Na Kwarai a Kasar Nan na Shekaru 24 ne ya Tsundumata Halin da Muke Ciki

Wani mazaunin kauyen, Ibrahim Rarah, ya ce sun ƙirga gawarwakin 'yan ta'adda akalla 16 a daya daga cikin wuraren da sojojin suka kai samame.

Da aka tuntube shi, kakakin rundunar yan sanda na jihar, DSP Sanusi Abubakar, ya ce ba'a sanar da shi ba a hukumance amma zai bincika kafin da dawo ga manema labarai.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa Legit.ng Hausa cewa tabbas lamarin ya faru kuma sun ji dadi sosai da wannan nasara saboda yadda suka addabesu.

Mutumin mai suna Malam Shamsu Haruna ya faɗa wa wakilinmu cewa:

"Eh tabbas, gaskiya ne Sojoji sun kashe yan bindiga da yawa, ban je wurin ba amma abinda ya faru sun kawo hari da daddare, aka sanar da Sojoji suka fatattake su."
"Washe gari sai suka dawo, to nan ne fa sojoji suka bi su har da jirage aka kakkashe su da yawa, wasu sun je wurin, mutane sun ji dadin abinda ya faru."

Kara karanta wannan

Adamawa 2023: Sanata Aishatu Binani Ta Yi Magana Mai Jan Hankali Game da Burinta Na Zama Gwamna

A cewarsa yana da wani aboki a kauyen dake makwaftaka da su kuma ya tabbatar masa cewa yan ta'addan sun shiga garinsu a ranar.

'Yan Sanda Sun Kama Makamai a Zamfara

A wani labarin kuma Yan sanda sun cika hannu da wata mata da namiji dauke da daruruwan alburusai da bindiga a Zamfara

Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan Zamfara, Muhammad Shehu, ya ce wadan da ake zargin sun amsa laifin kaiwa yan bindigan Jeji makamai.

Shehu ya kara da cewa Emmanuel Emmanuel da wata mace mai suna, Nana Ibrahim, an kama su dauke da Alburusai 325 da bindigar AK-47 guda ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel