Zan Sauya Sa'ar Jihar Adamawa Idan Na Zama Gwamna, Sanata Binani

Zan Sauya Sa'ar Jihar Adamawa Idan Na Zama Gwamna, Sanata Binani

  • Yar takarar gwamna a jihar Adamawa ta jam'iyyar APC, Aishatu Binani, ta ci gaba da yawon neman kuri'un jama'a gabanin zabe
  • A karamar hukumar Toungo, Binani ta sha alwashin sauya sa'a da tattalin arzikin jihar Adamawa idan ta samu nasara
  • Manyan jiga-jigan APC da suka halarci gangamin kamfen sun ja hankalin mutane su kafa tarihi a siyasar Najeriya

Adamawa - 'Yar takarar gwamna a jihar Adamawa, karkashin inuwar APC, Sanata Aishatu Ɗahiru Binani, ta fara yawon neman zabenta a sassan jihar dake arewa maso gabashin Najeriya.

Sanata Binana ta yi jawabi mai jan hankali kuma takaitacce game da manufarta ga Adamawa yayin da jirgin yakin neman zabenta ya dira karamar hukumar Toungo jiya Talata.

Sanata Aishatu Binani.
Zan Sauya Sa'ar Jihar Adamawa Idan Na Zama Gwamna, Sanata Binani Hoto: dailytrust
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Aishatu Binani ta sha alwashin yin amfani da kwarewarta da gogewa a siyasa wurin sauya sa'ar jihar Adamawa, mutane su samu walwala.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban PDP, Dan Majalisa da Wasu Kusoshi Sun Bar Tafiyar Atiku, Sun Koma Kwankwaso

Tace zata yi amfani da hanyar da take da su a siyasa wajen sauya sa'a da tattalin arzikin jihar Adamawa idan har mazauna suka sahale mata kuri'unsu ta zama gwamna.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bisa haka ta yi kira ga masu kaɗa kuri'a da su zabi 'yan takarar jam'iyyar APC tun daga matakin shugaban kasa har zuwa Kansila domin su sha romon demokaradiyya.

Da yake hawabin a wurin taron, jigon APC kuma babban dan siyasa, Alhaji Mansor Toungo, ya tabbatar wa Binani cewa tana da goyon bayan mutanensa.

Ya kuma bukaci dandazon magoya bayansa a duk inda su ke su zabi Sanata Binani a zaben gwamna da ke tafe a watan Maris.

Hon. Abdulrazaq Namdaz, Mamban majalisar wakilan tarayya daga jihar Adamawa, ya ce:

"Al'ummata, Sanata Binani zata kafa tarihi a jihar mu a matsayin mace ta farko da zata zama zababbiyar gwamna idan Allah ya so, ku zabeta."

Kara karanta wannan

Ana Gab da Zabe, Dubbannin Jiga-Jigan APC a Mahaifar Babban Ministan Buhari Sun Koma PDP

Idan baku manta ba, shugagan kasa, Muhammadu Buhari, ya halarci kamfen Adamawa inda ya bayyana cikakken goyon bayansa ga Binani, kamar yadda This Day ta ruwaito.

Saura Kiris Na Zabi Wanda Zan Marawa Baya - Wike

A wani labarin kuma Gwamnan Ribas kuma jagoran gwamnonin G-5 ya bayyana matakin da suke game da wanda zasu goyi baya a 2023

Da yake jawabi a wurin Ralin yakin neman zaben PDP a jihar Ribas, Wike ya roki mazauna jihar su kaɗa wa PDP kuri'u a zaben gwamna da yan majalisu.

Game da zaben shugaban kasa kuwa, gwamnan ya nemi mutane su kara hakuri nan da ɗan lokaci kankani zasu san wanda ya kamata su jefa wa kuri'arsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel