Malami da Matarsa Sun Mutu Yayin Kokarin Ceto Dansu Daga Nutsewa a Ruwa

Malami da Matarsa Sun Mutu Yayin Kokarin Ceto Dansu Daga Nutsewa a Ruwa

  • Idan ajali ya yi kira dole a tafi, wani Fasto da matarsa sun mutu yayin da suka kaiwa dansu Agaji a cikin Teku
  • Bayanai sun nuna cewa ma'auratan yan kasar Brazil sun gamu da Ajalinsu ne daga shiga ruwan don taimaka wa yaron
  • Babban dan Mamatan yace kafin faruwar lamarin da kwana 2 ya haɗu da iyayensa a she karo na karshe kenan

Wani Malamin Coci a kasar Brazil, Felisberto Sampaio, tare da mai dakinsa, Inalda, sun rasa rayuwarsu yayin da suka yi kokarin ceto ɗansu mai shekara 13, Ian, daga nutsewa a ruwa.

Iyalan gidan Faston sun fita zuwa bakin Tekun Camacari da ke João Pessoa, jihar Paraiba domin shakatawa sai dai fitar ta koma takaici yayin da suka hangi ɗansu a ruwa yana fafutukar neman tsira.

Felisberto Sampaio.
Malami da Matarsa Sun Mutu Yayin Kokarin Ceto Dansu Daga Nutsewa a Ruwa Hoto: punchng
Asali: UGC

Jaridar Punch ta ruwaito cewa a kokarin kubutar da ɗansu, ma'auratan ba tare da tunanin komai ba suka yi tsalle suka fada Tekun domin ceto yaron.

Kara karanta wannan

Ana Gab da Zabe, Dubbannin Jiga-Jigan APC a Mahaifar Babban Ministan Buhari Sun Koma PDP

Bisa rashin sa'a, iyayen biyu ba su iya zuwa wurin da ɗansu yake neman Agaji ba. Wasu masu kamun Kifi ne suka yi nasarar tsamo yaron daga ruwa tare dan gidan Faston.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga baya masu kamun kifin suka koma nemo Malamin da matarsa, suka dauko su a cikin dan Kwale-kwalensu zuwa bakin gabar Tekun.

Bayan fito da su, bayanai sun nuna cewa sai da ma'aikatan jinya suka sanya Fasto Filiberto, dan kimanin shekara 43 da matarsa mai shekaru 42 a cikin CVR domin ceton rayuwarsa.

Sai dai duk da haka daga baya Likitocin suka tabbatar da cewa ma'auratan sun riga mu gidan gaskiya, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ranar Talata 10 ga watan Janairu, 2023. Babban dan mamatan, Isaac ya ce ranar 8 ga watan Janairu ya ga iyayensa bai san haɗuwarsu ta karshe kenan ba.

Kara karanta wannan

Kyakkyawar Budurwa Da Ta Samu Miji Bature a Soshiyal Midiya Ta Yi Murnar Cika Shekaru 4 Da Aurensu

Wata Mata Ta Nuna Farin Ciki da Ganin Danta Ya Kwanta da Yar Aiki

A wani labarin kuma Wata Mata Ta Nuna Farin Ciki a Bidiyo Lokacin Da Ta Kama Yar Aiki Ta Kwanta da Ɗanta

Wata mata ta haddasa cece-kuce a Soshiyal midiyan bayan ta bayyana abinda ta ga yar aikinta na yi da ɗan ƙaramin ɗan da ta haifa a kan gadon dakinta.

Matar mai suna Massey, wacce ke rayuwa a gidanta. ta nuna jin daɗinta game da yadda 'yar aiki ke kaunar ɗanta kuma ta roki Allah ya albarkaci matar saboda halaccin da take mata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel