Jiga-Jigan APC a Mazabar Ministan Buhari Sun Sauya Sheka Zuwa PDP

Jiga-Jigan APC a Mazabar Ministan Buhari Sun Sauya Sheka Zuwa PDP

  • Jam'iyar APC ta gamu babban cikas a Benuwai ana tsaka da kamfe yayin da dubbannin mambobi suka sauya sheka zuwa PDP
  • Masu sauya shekar sun fito ne daga karamar hukuma ɗaya da Sanata George Akume, tsohon gwamnan jihar Benuwai
  • Akume a yanzu haka shi ne Ministan ayyuka na musamman aa gwamnati mai ci karkashin shugaba Buhari

Tarka, Benue - Dubannin mazauna mahaifar tsohon gwamnan jihar Benuwai, Sanata George Akume, sun tattara kayansu sun bar jam'iyyar APC zuwa PDP ranar Litinin 16 ga watan Janairu, 2023.

Yanzu haka Sanata Akume ne ministan ayyuka na musamman da harkokin alaka da gwamnatoci a gwamnatin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Taron PDP a Benuwai.
Jiga-Jigan PDP a Mazabar Ministan Buhari Sun Sauya Sheka Zuwa PDP Hoto: Benue PDP
Asali: Facebook

Jam'iyyar PDP mai mulkin jihar ta karbi tuban masu sauya shekar a mahaifar ministan Wannune da ke karamar hukumar Tarka, jihar Benuwai.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban PDP, Dan Majalisa da Wasu Kusoshi Sun Bar Tafiyar Atiku, Sun Koma Kwankwaso

Wannan ci gaban na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun PDP na jihar kuma kakakin kwamitin kamfe, Bemgba Iortyom, ya turo ma Legit.ng Hausa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa yan siyasan suka koma PDP?

Da yake jawabi a madadin sauran masu sauya sheka, Honorabul Dennis Tser wanda aka fi sani da Baba Danny yace sun gaji da abubuwan dake faruwa a APC.

"Mun gaji da zama wurin da babu sakamako a siyasa, wurin da Akume kadai sai iyalansa suke amfana suna kara ƙiba yayin da saura kuma ke shan baƙar wahala."

Yayin kare ikirarinsa, Baba Danny ya tuna abinda ya faru a baya bayan nan wanda Akume ya ƙakaba matarsa a matsayin yar takarar APC a mazabar Gboko/Tarka a majalisar tarayya.

Ya kuma kara tono lokacin da Akume ya nada kansa da mai ɗakinsa, Regina Akume a matsayin Deleget na ƙasa daga yankin Tarka a zaben fidda dan takarar shugaban kasa na APC.

Kara karanta wannan

Saura Yan Makonni Zabe, Atiku da PDP Sun Yi Babban Rashi a Arewacin Najeriya

A cewarsa duk wannan shaida ce da ke nuna kama karya da maida jam'iyya tankar wata kadararsa ta kai da kai.

Wani daga cikin masu sauya shekan da ya yi jawabi a wurin taron yace abinda ya kamata a kira APC reshen jihar Benuwai shi ne, "Kamfanin Akume na kashin kansa."

Tsoffin Masu Neman Takara a PDP 8 Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Zamfara

A wani labarin kuma Saura Yan Makonni Zabe, Atiku da PDP Sun Yi Babban Rashi a Arewacin Najeriya

Kwanaki kasa da 40 gabanin zaben shugaban kasa a watan Fabrairu, wasu manyan kusoshin jam'iyar PDP a Zamfara sun bar tafiyar Atiku.

The Nation tace jiga-jigan sun nemi takara da zabukan fidda gwamnin PDP na majalisun tarayya kuma sun samu tarba hannu bibbiyu daga shugaban APC na jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel