'Tana Kaunarsa' Wata Mata Ta Nuna Farin Ciki ɗa Ganin Danta Ya Kwanta da Yar Aiki

'Tana Kaunarsa' Wata Mata Ta Nuna Farin Ciki ɗa Ganin Danta Ya Kwanta da Yar Aiki

  • Wata mata ta haddasa cece-kuce bayan ta bayyana abinda ta ga yar aikinta na yi da ɗan ƙaramin ɗan da ta haifa
  • Matashiyar budurwar mai suna Atieno Massey ta shiga ɗakinta kawai sai ta ga yar aiki na kwance tana bacci tare da ɗanta
  • Hakan ya zo mata da mamaki kuma ta shiga wani yanayi da ganin kulawar yar aikin ke wa yaton, mutane sun tofa albarkacin bakinsu

Wata mata da har yanzu bata samu miji ta yi aure ba, Atieno Massey, ta yi kalaman yabo ga matar da take mata aiki a gida yayin da ta saki Bidiyon matar tare da ɗan karamin ɗanta.

Massey ta nuna jin daɗinta game da yadda 'yar aiki ke kaunar ɗanta kuma ta roki Allah ya albarkaci matar saboda halaccin da take mata.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Babbar Mota Ta Murkushe Motocin Ayarin Gwamnan Arewa, Ya Sha Da Kyar

Massey.
'Tana Kaunarsa' Wata Mata Ta Nuna Farin Ciki ɗa Ganin Danta Ya Kwanta da Yar Aiki Hoto: @atienomassey
Asali: UGC

A wani Bidiyo da ta saki a shafin TikTok, Massey ta bayyana cewa ta shiga ɗaki kenan sai ta hangi yar aiki da kuma ƙaramin yaron suna kwance a gado suna bacci tare.

Da take ba da amsar wasu sakonni, Massey ta ce zancen gaskiya har yanzun bata yi aure ba kuma tana rayuwa ne daga ita sai ɗanta sai kuma wannan yar aiki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamanta tace:

"Gayu ina godiya da yadda kuka faɗi ra'ayoyinku amma a zahirin gaskiya ban kai ga yin aure ba, ina zaune ne da wannan yar aiki kamar yar uwata saboda tana ƙaunar yaron da na haifa."

Kalli bidiyon anan

Yadda mutane suka faɗi ra'ayoyinsu a shafin

user329454631596 tace:

"Rayuwa kala biyu ce, idan ka kula da mai maka aiki yadda ya kamata, zata kula da ɗanka kuma ta yi aikinta, rayuwa ka yi ne a maka."

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: ASUU za ta sake komawa yaji aiki saboda wasu dalilai

wennyotobi ta ce:

"Allah ya haɗa ni da kamar wannan yar aikin, ba zan lamurci son jiki ba amma idan kika kulamun da ɗa na ba wani abu."

Jaquiline Gwanzura tace:

"Abinda na sani a koda yaushe yana faruwa shi ne 'yar aiki na kula da ɗan masu gida ne yadda ake kula da ita, abinda ta yi yana bayanin halinki ne. Allah ya miki Albarka."

A wani labarin kuma Wani yaro ya sauya bayan lashe wata gasa, ya tashi daga Kwandastan Mota kuma ya haɗu da fitaccen Attajiri

Watanni da dama da suka wuce, Adeoye Fawaz, ya kasance mara galihu a jihar Lagas inda yake kwana a karkashin gadar Oshodi.

Matashin ya shahara ne bayan ya lashe gasar wasan 'chess' kuma nan take dai mutane suka mayar da hankali ga labarin yadda yake rayuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel