Budurwa Ta Rabu da Attajirin Saurayinta, Ta Auri Mai Nakasu, Bidiyon Ya Yadu

Budurwa Ta Rabu da Attajirin Saurayinta, Ta Auri Mai Nakasu, Bidiyon Ya Yadu

  • Wata kyakkyawar budurwa, Polu Mukami, ta kawo karshen soyayyarsu da attajirin saurayina don auren wani mutum mai nakasu
  • Poly ta bayyana yadda ta fara ganin nakasasshen mutumin wanda ta fada tarkon sonsa a ganin farko
  • Duk da tarin kalubale da rashin amincewar dangi da rashin kudi, ma'auratan suna rayuwarsu ba tare da danasani ba

Wata matashiyar budurwa, Poly Mukami, ta bayyana cewa tana da wani saurayi mai kudi a lokacin da ta fara ganin mijinta, John Masharia.

Poly ta amsa tayin auren John wanda bai da hannu kuma ta ce bata yi danasanin wannan shawara da ta yanke ba.

Mata da miji
Budurwa Ta Rabu da Attajirin Saurayinta, Ta Auri Mai Nakasu, Bidiyon Ya Yadu Hoto: YouTube/Afrimax
Asali: UGC

Da take zantawa da Afrimax, matashiyar wacce dangi da kawaye basu yi na'am da aurenta ba ta bayyana cewa soyayya ce a ganin farko.

Ta ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Kyakkyawar Budurwa Da Ta Samu Miji Bature a Soshiyal Midiya Ta Yi Murnar Cika Shekaru 4 Da Aurensu

"Ganin farko da na yi masa, soyayyace ta sace zuciyata. Na yi mamaki. Na kasa yarda cewa wani mutum zai iya amfani da kafarsa ya yi abubuwa kamar shan shayi. Na tunkare shi don sanin yadda yake aikata hakan.
"Mun dan yi hira kadan wanda ya kare da musayar lambobin waya. Karfin gwiwarsa ya matukar burge ni."

John ya ce bai taba neman Poly ta yi soyayya da shi ba

Da aka tambaye shi game da soyayyarsu, John ya bayyana cewa bai taba neman Poly ta yi soyayya da shi ba.

"Ban taba neman ta yi soyayya irin wacce aka saba da ni ba. Kai tsaye na fada mata abun d nake so. Na nemi aurenta kuma ta saurare ni ba kamar sauran mata da basa bani dama ba. Na fada mata duk tarihin rayuwata kuma hakan ya yi mata."

Ya jinjina maka kan son shi da ta yi da kuma amsarsa hannu bibbiyu.

Kara karanta wannan

Matashi ya Lakadawa Mahaifiyarsa Dukan Kisa Kan Rabon Gado, Tace ga Garinku a Delta

"A kodayaushe tana karfafa mun gwiwar zama jajirtaccen mutum.
"Ina mai godiya a gareta saboda ta so ni kuma ta karbe ni a yadda nake.
"Hatta lokacin da ba ni da kudin siyan abinci ko biyan haya, tana karfafa mun gwiwa sannan ta tunatar da ni cewa muna tare. Ta sadaukar da abubuwa da dama a gareni kuma ina gode mata a kan haka."

Poly ta ce ta ki amsa tayin masoyanta da dama saboda John

Poly ta kuma bayyana cewa attajirin saurayinta ba shi kadai ne mutumin da ta ki yarda da shi ba don kasancewa da John.

"Na kasance da maza da dama da suka yi kokarin shawo kaina. A lokacin da na hadu da John, ina da wani saurayi wanda kawayena da dama sun san shi. Duk sun yi kokarin lallaba ni na aure shi tuna yana da kudi da kyau.
"A lokacin da na fada ma kawayena cewa John na zaba, sun kasa yarda da hakan. Sun yi mani tambayoyi da dama da karfafa mani gwiwa."

Kara karanta wannan

Sabon Ango ya kori Mahaifiyarsa Daga Gidansa Bayan Kwana 2 da ta Kai Ziyara, Yace Marar Masa Mata Tayi

Kalli bidiyon a kasa:

Matashi na neman auren mata ta biyu, ya ce ba zai yi lefe ba

A wani labarin kuma, wani Bakatsine ya nuna sha'awarsa na son kara auren mata ta biyu inda ya yi alkawarin biyan sadaki naira miliyan daya.

Sai dai kuma ya ce baya son kayan daki da na kicin haka shima ba zai yi kayan lefe ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel