Ba Na Son Mace Mai Kiba: Matashi Na Neman Mata Ta Biyu, Ya Ce Zai Biya Sadaki N1m

Ba Na Son Mace Mai Kiba: Matashi Na Neman Mata Ta Biyu, Ya Ce Zai Biya Sadaki N1m

  • Wani matashi dan Najeriya wanda ke da matar aure daya ya nuna sha'awarsa na son kara auren ta biyu
  • Matashin mai shekaru 49 wanda ya fito daga jahar Katsina ya gindaya wsu sharudda da yake son matar ta cika kafin ayi auren
  • Daga cikin abubuwan da ya shimfida shine cewa zai biya sadaki naira miliyan 1 da kuma N200k toshiyar bakin hotunan kafin aure

Wani matashi dan Najeriya ya nuna sha'awarsa na son kara auren mata ta biyu kuma tuni ya bude kafar yin hakan domin mata da ke ra'ayinsa su bi layi ya zabi daya.

Mutumin wanda ya fito daga jahar Katsina kuma ma'aikacin gwamnati ya jero abubuwan da yake so matar da aura ta kasance da su.

Neman karin aure
Ba Na Son Mace Mai Kiba: Matashi Na Neman Mata Ta Biyu, Ya Ce Zai Biya Sadaki N1m Hoo: MoMo Productions, Twitter/@Halal_Match
Asali: Getty Images

A cewar wani dandalin kulla aure na Musulunci, Halal Match wanda ya wallafa bayanin a Twitter, mutumin na zaune a Lagas yanzu haka.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya Sun Zagaye Mai Kama Da Shugaba Buhari a Wani Bidiyo Da Ya Yadu

Matashin wanda ya mallaki kwalin digiri yana son mace bazawara mai aiki tsakanin shekaru 30 zuwa 35, wacce ke da addini kuma mara kiba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sharuddan auren shine zai biya sadaki naira miliyan daya da N200,000 toshiyan bakin hotunan kafin aure. Kuma ya ce baya son gagarumin biki, baya son kayan daki da kicin daga bangaren matar.

Hakazalika mutumin Musulmi ne.

Kalli wallafarsa a kasa:

Jama'a sun yi martani

@khaleelabba ya ce:

“Bazawara yake so. Don haka ku je ku ta neman kananan yara marasa aure. Wannan bai isa adalci ba?”

@AliHuss70629085 ya ce:

“Toshiyar bakin dina da hotunan kafin aure! Ban ga amfanin haka ba, domin rashin yin dina zai Hana su saba wa Allah.”

@Mansur_N_A ya ce:

“Na so tsarinsa, ya fadi abun da yake so kai tsaye don gudun dirama mara amfani a gaba...”

Kara karanta wannan

Ina Biyan Kudin Haya N800k Duk Shekara: Budurwa Ta Nuna Cikin Dakinta Da ke Da Wuta 24/7

@hosnideedat ya ce:

“OMO Allah kadai ya san yan mata nawa ne suka zama bazawara....mata da kudi na tabbata yan mata 200 sun rigada sun nuna sha’awa.”

A soshiyal midiya muka hadu, matashiya ta yi murnar cika shekaru 4 da Baturen mijinta

A wani labarin kuma wata matar aure ta je shafin soshiyal midiya don murnar cikarsu shekaru hudu da aure ita da Baturen mijinta.

Matar wacce ta cika da farin ciki ta ce sun hadu ne a wani dandalin kulla soyayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel