A Kan Gado, Matashi Yayi wa Mahaifiyarsa Dukan Kawo-Wuka, Ta Sheka Lahira

A Kan Gado, Matashi Yayi wa Mahaifiyarsa Dukan Kawo-Wuka, Ta Sheka Lahira

  • Wani matashin 'dan Najeriya mai rabon a yi ya masge mahaifiyarsa a yankin Umusam Ogeb da ke Kwale a jihar Delta inda ta sheka lahira
  • An gano cewa, wata kadararsu suka siyar ita da 'dan ta daya tilo amma yadda tace a raba kudin ne bai gamsar da shi ba, lamarin da ya kawo hatsaniyar
  • Tuni dai makwabta suka damke matashin tare da mikasa hannun 'yan sa kan yankin inda daga bisanai aka kai shi caji ofis din Kwale

Delta - Wani matashi 'dan Najeriya ya lakadawa mahaifiyarsa dukan tsiya har ta rasa ranta a jihar Delta, tuni kuwa hukumar 'yan sanda suka cafkesa.

Lamarin ya faru ne a Umusam Ogbe da ke Kwale a jihar Delta ta kudancin Najeriya kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sabon Ango ya kori Mahaifiyarsa Daga Gidansa Bayan Kwana 2 da ta Kai Ziyara, Yace Marar Masa Mata Tayi

'Dan Sanda
A Kan Gado, Matashi Yayi wa Mahaifiyarsa Dukan Kawo-Wuka, Ta Sheka Lahira. Hoto daga leadership.ng
Asali: UGC

An tattaro yadda matashin da ya dawo daga Legas kuma 'da daya tilo wurin mahaifiyarsa ya taimaka wurin siyar da kadararsu ta gado.

A sanadin hakan ne hatsaniya ta barke tsakaninsa da mahaifiyarsa kuma ana tsaka da hakan ne ya doke ta ta fadi ta mutu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kamar yadda ganau ya rahoto:

"Bayan iyalan sun amince da siyar da kadararsu, musu ya harke kan yadda za a raba bayan an siyar. Matsayar mahaifiyar bata yi daidai da ta yaron ba. A wannan lokacin ne ya doke ta kuma ta fadi ta mutu.
"Cike da rashin sa'a, makwabta sun gaggauta kama shi tare da hana shi tserewa kamar yadda yayi niyya inda suka mika shi hannun 'yan sa kai da ke wurin."

Tuni 'yan sa kan suka cafke shi tare da mika shi caji ofis hannun 'yan sandan yankin Kwale wadanda suka je har inda abun ya faru suka dauke gawar matar.

Kara karanta wannan

Matasa Sun Halaka Basarake a Jihar Arewa, Gwamna Ya Kakaba Dokar Zaman Gida

A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe, ya tabbatar dafaruwar lamarin inda yace ana cigaba da bincike a kai.

Ango ya fattaki mahaifiyarsa daga gidansa bayan ta tsinkawa amarya mari

A wani labari na daban, wani sabon ango 'dan Najeriya ya kori mahaifiyarsa daga gidansa bayan kwana biyu kacal da tayi.

Ya bayyana cewa ta marar masa amarya ne kuma ya so fahimtar da ita amma ta ki ganewa, don haka yace ta bar masa gidansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel