Malamai a Kasashen Ingila da Wales Sun Sanar da Shiga Yajin Aikin Rashin Albashi

Malamai a Kasashen Ingila da Wales Sun Sanar da Shiga Yajin Aikin Rashin Albashi

  • Malaman makaranta a kasar Burtaniya za su shiga yajin aiki saboda rashin samun karin albashi na wata-wata
  • Wannan lamari dai na zuwa ne daidai lokacin da wasu ma'aikatan a wasu hukumomi ke ci gaba da yajin aiki
  • An ce wannan yajin aikin zai shafi kusan dukkan makarantu domin ankarar da gwamnati halin da malamai ke ciki

Burtaniya - An samu tsaiko a Burtaniya yayin da wata babbar kungiyar malaman makaranta ta bayyana shiga yajin aikin kwanaki saboda rashin samun albashi yadda suke so a wata mai zuwa a Ingila da Wales.

Kungiyar mai suna National Education Union (NEU) ta ce mambobinta sun yanke shawarin shiga yajin aikin ne a matsayin daya daga hanyoyin da za su bi don jawo hankali gwamnati ta kara albashi duba da hauhawar farashin kayayyaki.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Babban Banki Ya Koma Bakin Aiki, CBN Ya Fitar da Sabuwar Sanarwa

Wannan sanarwa dai na zuwa ne daidai lokacin ma'aikatan gwamnati ke ci gaba da guna-guni kan a kara musu albashi saboda tsadar kayayyaki da ake fuskanta a kasar, Daily Trust ta ruwaito.

Turawa sun shiga yajin aiki saboda kudin albashi
Malamai a Kasashen Ingila da Wales Sun Sanar da Shiga Yajin Aikin Rashin Albashi | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A cewar sakataren kungiyar, Kevin Courtney:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Mun yi imani da cewa, gwamnati ta san akwai bukatar gyara albashin malamai."

Za a zauna da ministan ilimi

Hakazalika, an ce shugabannin kungiyar za su gana da minsitan ilimi a kasar a ranar Laraba mai zuwa, BBC News ta ruwaito.

Mary Bousted, daya daga cikin sakatarorin kungiyar ta shaida cewa:

"Sun san da gaske muke. Sun san a shirye kuke ku dauki matakin kare ayyukanku, ku kare albashinku da kudaden da kuke kashewa da kuma kare damar ci gaba da aikin."

Kungiyar ta ce wannan yajin aiki zai fara ne daga ranar 1 ga watan Fabrairu a kasar baki daya, kana za a yi wasu kwanakin kauracewa aiki a cikin watannin Fabrairu da Maris.

Kara karanta wannan

2023: Dubbannin 'Yan SPW Sun Yanke Shawara, Sun Fadi Wanda Zasu Goyi Baya Tsakanin Tinubu da Atiku

Ta yaya hakan zai shafi ikimi?

A cewar kungiyar, wannan yajin aikin dai zai shafi kowacce makaranta ne na tsawon kwanaki hudu.

Hakan zai haifar da damuwa ga iyaye, wadanda a baya suka fuskanci matsaloli saboda annobar Korona da ta yi barna a shekarun baya.

Ba wannan ne karon farko da aka samu faruwar yajin aiki a kasar Burtaniya bam an yi hakan a watan Disamban bara da ma dai wasu lokuta da aka samu yajin aikin ma'aikatan lafiya.

A shekarar da ta gabata, malaman jami'a sun shiga yajin aiki a Burtaniya, lamarin da ya jawo cece-kuce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel