Kamar a Najeriya, Malaman Jami’a sun yi yajin-aiki a Birtaniya, su na kuka da Gwamnatinsu

Kamar a Najeriya, Malaman Jami’a sun yi yajin-aiki a Birtaniya, su na kuka da Gwamnatinsu

  • Ma’aikatan jami’a da dama sun fita kan titi su na zanga-zanga daga farkon makon nan a Birtaniya
  • Kungiyar ma’aikatan jami’a ta UCU a kasar Ingila ta na kuka a kan karancin albashi, tsarin fansho
  • Dalibai sun ba ma’aikatan kwarin gwiwa, su na raba masu kayan abinci yayin da suke zanga-zanga

United Kingdom - Dubban ma’aikatan jami’a a kasar Birtaniya sun shiga yajin-aiki a makon nan. BBC ta ce ma’aikatan su na kuka ne a game da hakkokinsu.

Kamar yadda mu ka samu labari, za a shafe akalla kwanaki goma ana wannan yajin-aiki a Ingila.

Ma’aikatan jami’a sun bukaci gwamnatin Birtaniya tayi wani abu a game da karancin albashinsu da kuma yawan zaftare masu kudin fansho da hukuma ke yi.

Kara karanta wannan

ASUU: Ba dole sai an shafe wata ba, a kwana 7 za mu dawo aiki idan Gwamnati ta ga dama

Ma’aikatan su na kukan akwai zalunci a sabon fansho da aka kawo. Ana zargin tsarin USS da aka shigo da shi zai sa malaman su tashi wayam idan sun yi ritaya.

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar UCU ta ma’aikatan jami’a a kasar Ingila ta na neman a karawa ‘ya ‘yanta akalla fam £2,500 (N1.41m) a albashin na su.

Malaman Jami’a
Ma’aikatan jami’an Birtaniya a titi Hoto: www.telegraph.co.uk
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu daga cikin bukatun ma’aikatan sun hada da kiran a daina lafta masu ayyukan da ya fi karfinsu.

Yadda za ayi yajin-aikin

Za a raba yajin-aikin na kwanaki goma zuwa makonni uku. A makon farko za ayi zanga-zanga a kan batun fansho. Yajin-aikin zai yi tasiri a jami’o’i fiye da 40.

Bayan makon farko, ma’aikatan za su yi tattaki a ranakun 21 da 22 na Fubrairu a makarantu 68 domin su nemi a kara masu albashi da sauran hakkokin aiki.

Kara karanta wannan

Yajin-aiki: Kungiyar Dalibai ta fadi matakin da za ta dauka kan ASUU da Gwamnatin Buhari

A makon karshe na yajin-aikin, za a dauki kwanaki uku ranar karshe na watan Fubrairu zuwa ranar 2 ga watan Maris ba tare da bude wasu jami’o’in kasar ba.

Dalibai su na goyon bayansu

Jaridar Daily Mail ta fitar da rahoto cewa an samu wasu dalibai da suke goyon bayan malaman jami’an da ke yajin-aiki, ta hanyar raba masu kek da kuma biskit.

Ma’aikatan jami’a fiye da 50, 000 suka fito tituna su na zanga-zanga a fadin jami’o’i 44 a Birtaniya yayin da aka shiga wannan yajin-aiki a ranar Litinin da ta wuce.

Ana yajin-aiki a Najeriya

A halin yanzu an rufe jami'o'in gwamnati a kasar nan, amma wani jagora na kungiyar ASUU ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta iya takaita yajin-aikin na su.

Dr. Christopher Piwuna ya ce malaman jami’a na iya janye yajin-aiki idan gwamnatin tarayya ta yi abin da ya dace, ya cika duk alkawuran da ta yi wa kungiyar ASUU.

Kara karanta wannan

Za a kara laftawa Gwamnatin Buhari ciwon kai, Kungiyar NUPENG na shirin yajin-aiki

Asali: Legit.ng

Online view pixel