Amarya Ta Rasa Ido Daya a Wajen Shagalin Bikinta a Kano

Amarya Ta Rasa Ido Daya a Wajen Shagalin Bikinta a Kano

  • Wasu mutane da ake zargin yan bijilante ne sun farmaki wajen wani shagalin bikin da aka yi a garin Kano a ranar Lahadi
  • An tattaro cewa yan dokar sun hau mutane da duka a wajen inda suka jefi amarya da dutse wanda ya yi sanadiyar lahanta mata ido daya
  • Rundunar yan sandan jahar Kano ta tabbatar da faruwar al'amarin inda ta damke mutane biyu

Kano - Wata Amarya mai suna Khadija Abdullahi ta hadu da mummunan kaddara inda ta rasa ido daya a wajen shagalin bikinta a jihar Kano.

Mummunan al'amarin ya afku ne a ranar Lahadi lokacin da wasu yan bijilanti suka farmaki wajen liyafar da amayar da kawayenta suka shirya.

Jihar Kano
Amarya Ta Rasa Ido Daya a Wajen Shagalin Bikinta a Kano Hoto: The Nation
Asali: UGC

Rahotanni sun kawo cewa yan bijilanti din sun fara dukan duk wanda suka gani a wajen ciki kuwa harda amaryar. A nan ne suka bugawa amaryar dutse,

Kara karanta wannan

Jerin Matsaloli Jingim da ke Jiran Duk Wanda Zai Gaji Shugaba Buhari a Aso Rock

Khadija ta zargi yan dokar da lalata mata rana mafi daraja a rayuwarta inda ta nemi a kwato mata yancinta, rahoton allnews.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rundunar yan sandan jihar Kano ta yi martani

A halin da ake ciki, rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da faruwar al'amarin inda ta ce tuni ta kama mutane biyu da ake zargin suna da hannu a ciki, sashin Hausa na BBC ya rahoto.

Rundunar yan sandan ta kuma ce za a gurfanar da wdanda aka kama a gaban kotun majistare da ke jihar.

Ba za mu amince da wannan lamari ba, ango

Har ila yau, angon amaryar da aka yi wa lahani mai suna Mustapha Bala ya ce ba za su amince da abin da aka yi mata ba.

Ya ce bai ji dadin wannan al'amari da ya faru be saboda a ranar da ya je gida kasa bacci ya yi saboda yadda yaga tana kuka.

Kara karanta wannan

Sharri aka min: Dan sandan da bindige lauya mai juna biyu ya musanta zargin kisa

Ya kuma ce an daura masu aure kuma zai zauna da ita a haka don shi ya yarda da kaddara.

Legit.ng ta tuntubi wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa inda ya ce an hana kidan DJ a unguwar ita kuma amaryar ta yi.

Ya ce:

"An hana kiɗan DJ a unguwar, ita kuma ta yi, kuma kafin ranar, sun ce mata kar ta yi."

Uwa ta koka kan dabi'ar diyarta budurwa na yin bacci a dakin danta

A wani labari na daban, wata uwa ta koka kan yadda matashiyar diyarta ke da dabi'ar zuwa kwanciya a dakin dan uwanta maimakon a nata dakin.

Uwar ta nemi jama'a su bata shawara a kan yadda za ta shawo kan al'amarin wanda ke matukar damunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel