Ina Bukatar Taimako: Uwa Ta Koka Bayan Kama Diyarta Budurwa Tana Bacci a Dakin Danta

Ina Bukatar Taimako: Uwa Ta Koka Bayan Kama Diyarta Budurwa Tana Bacci a Dakin Danta

  • Wata mata ta kasa gaskata idanunta bayan ta gano diyarta budurwa mai shekaru 15 tana bacci a dakin danta
  • Matar ta zata yarinyar na bacci ne a dakinta kasancewar ta gano ta kwance a dakin da tsakar dare
  • Mahaifiyar wacce ta shiga damuwa ta nemi shawarar jama'a kan yadda budurwar diyar tata za ta shawo kan wannan tsoro nata

Wata mata ta nemi shawara yayin da ta koka kan yadda diyarta budurwa bata iya bacci ita kadai da daddare.

Ta gano cewa tana bukatar taimako bayan ta sake kama diyar tata mai shekaru 15 tana bacci a dakin dan uwanta.

Budurwa da mahaifiyarta
Ina Bukatar Taimako: Uwa Ta Koka Bayan Kama Diyarta Budurwa Tana Bacci a Dakin Danta Hoto: TikTok/@queen_already1
Asali: UGC

Ta wallafa daya daga cikin irin wannan lokuta a TikTok. A bidiyon, an gano sanda ta shiga cikin dakin sannan aka gano ta tana bacci a lullube.

Kara karanta wannan

Ko da ne ga dan siyasa: Bidiyon mahaukaciyar da ta haifi jariri a kasuwa ya bar baya da kura

"Har sai yaushe diyata mai shekaru 15 za ta koyi bacci a dakinta ita kadai. A wannan ga'bar ina bukatar taimako" ta rubuta a bidiyon.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan ta tashi yarinyar, matar ta nemi ji daga gareta kan yadda aka yi ta dawo da kwanciya a dakin dan uwan nata.

"Na zata na tashe ki da tsakar dare sannan na ga kin shiga cikin dakinki don yin bacci. Me kuma kike yi a dakin Jaden?"

Da take watsi da magagin yarinyar, matar ta yi mamakin har sai yaushe ne wannan zai zo karshe."

"Wani irin wawanci ne wannan? Ki daina zuwa dakin dan uwanki kina bacci. Ki kawo karshen wannan tsoro naki," cewar mahaifiyar.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Dorata ce:

"Ba yadda za a shawo kan matsala irin wannan ba kenan ta hanyar katse mata baccinta da ihu, ki zaunar da ita ki yi mata magana sannan ki tambayeta matsalarta ba zancen shekaru bane."

Kara karanta wannan

Matashi ya Lakadawa Mahaifiyarsa Dukan Kisa Kan Rabon Gado, Tace ga Garinku a Delta

Richard ya ce:

"Kina bukatar ki zaunar da ita sannan ki tambayeta dalilin da yasa take kauracewa bacci a dakinta. Sannan ki duba irin fina-finan da take kallo ko labaran da take sauraro."

user3383552925908 ta ce:

"Na fara neman a bani sarari ina da shekaru 14 yadda nake jin dadin bacci ni kadai wasu lokutan na kan ji tsoron cewa idan na yi aure zai haifar da matsala."

Ikcon mama ta ce:

"Ba kowa ne ke iya bacci shi kadai ba. Na tuna lokacin da kanwata ta yi tafiya ta barni ni kadai ban ji ta dadi ba faaa."

A wani labari na daban, wata matar aure ta garzaya soshiyal midiya inda ta wallafa bidiyonta da na mijinta bature wanda suka hadu a dandalin sadarwa har ya kai su ga aure, yanzu shekarunsu hudu tare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel