Gobara Ta Tashi a Gidan Man AA Rano a Abuja, Babbar Fanka Ta Dauka

Gobara Ta Tashi a Gidan Man AA Rano a Abuja, Babbar Fanka Ta Dauka

  • Wani gidan man Fetur mallakin A.A Rano da ke kan Titin Lokoja-Abuja da kuma babbar Motar dakon mai a gidan sun kama da wuta
  • Rundunar yan sandan Abuja ta hannun mai magana da yawunta, ta ce jami'an kwana-kwana da yan sanda sun dira sun mamaye wurin
  • Josephine Adeh ta ce jami'an ba da agajin gaggawa na kokarin kashe wutar da kuma dakile rasa kadarorin al'umma masu yawa

Abuja - Gidan siyar da man Fetur mallakin fitaccen dan kasuwan nan, AA Rano da ke kan Babban Titin Lokoja-Abuja ya kama da wuta ranar Lahadi, 15 ga watan Janairu, 2023.

A wata sanarwa da rundunar yan sandan birnin tarayya Abuja ta fitar kuma wakilin jaridar Punch ya ci karo da ita, ta ce jami'an yan sanda da jami'an hukumar kwana-kwana sun isa wurin a kan lokaci.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Miyagu Sun Kai Farmaki Coci a Katsina, Sun Yi Garkuwa da Mutum 25

Matsalar Gobara.
Gobara Ta Tashi a Gidan Man AA Rano a Abuja, Babbar Fanka Ta Dauka Hoto: punchng
Asali: UGC

Jami'ar hulda da jama'a ta rundunar 'yan sandan Abuja, Josephine Adeh, ta ce Dakarun ba da agaji na hukumomi da dama sun isa wurin m domin kai ɗauki, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

A sanarwan, Adeh ta ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"An samu ibtila'in Gobara a gidan man A.A Rano. Wutar ta tashi ne yayin da babbar Tankar dakon Fetur ke sauke mai a gidan sayar da Fetur din."
"Jami'an rundunar 'yan sanda, jami'an hukumar kashe Gobara da sauran hukumomin ba da agajin gaggawa sun isa wurin domin dakile wutar da kashe ta."
"Ba ya ga kashe wutar jami'an ba da agajin zasu tabbata mutane ba su yi mummunan asara ba da rasa kadarori."

Jirgin Sama Dauke da Mutane Sama da 70 Ya Yi Hadari, Da Yawa Sun Rasu

A wani labarin kuma Wani jirgin sama da ya dauko Fasinjoji 72 ya gamu da hatsari a kasaɗ Nepal, mutane kusan 30 sun ce ga garinku nan

Kara karanta wannan

Matasa Sun Halaka Basarake a Jihar Arewa, Gwamna Ya Kakaba Dokar Zaman Gida

Wani jirgin sama dauke da fasinjoji da ma'aikata 72 ya yi hatsari a Nepal, akalla mutane 29 zuwa yanzu aka gano sun mutu. Wasu an kai su Asibiti.

Hukumomi a kasar sun ce ana ci gaba da kokarin kashe wutar da ta kama da kuma zakulo mutanen dake cikin jirgin. Firaminista ya kira taron gaggawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel