Karamin Yaro Ya Yiwa Likita Kallon Uku Saura Kwata Bayan Ya Tsira Masa Allura, Bidiyon Ya Ba Da Mamaki

Karamin Yaro Ya Yiwa Likita Kallon Uku Saura Kwata Bayan Ya Tsira Masa Allura, Bidiyon Ya Ba Da Mamaki

  • Wani bidiyo da ya yadu a manhajar TikTok ya nuno lokacin da aka yiwa wani karamin yaro allura a wani asibiti
  • Jim kadan bayan likita ya gama yi masa allura a hannu, sai yaron ya juya ya yi masa wani irin kallo na uku saura kwata ba tare da ya yi kuka ba
  • Mutanen da suka ci karo da bidiyon sun jinjinawa taurin rai da karfin zuciya irin na yaron

Wani karamin yaro ya baiwa mutane da dama a soshiyal midiya mamaki bayan ya nuna dakiya da taurin rai yayin da aka yi masa allura a wani asibiti.

A wani bidiyo da ya yadu, an gano yaron zaune a kan kafar mahaifiyarsa yayin da likita ke tsira masa allura a hannunsa.

Karamin yaro
Karamin Yaro Ya Yiwa Likita Kallon Uku Saura Kwata Bayan Ya Tsira Masa Allura, Bidiyon Ya Ba Da Mamaki Hoto: @xixi.lovelife/TikTok
Asali: UGC

Jama'a sun zuba ido don ganin yaron ya bare baki yana kuka yayin kallon bidiyon amma sai ya ba marada kunya.

Kara karanta wannan

Kyakkyawar Budurwa Ta Fada Tarkon Son Wani Boka, Ta Saki Zazzafan Bidiyonsu a Kogi

Maimakon haka, yaron ya nuna jarumta yayin da ya yiwa likitan kallon uku saura kwata bayan ya gama tsira masa alluran.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Yaron bai yi kuka ba bayan an masa allura. Kalli idonsa," kamar yadda rubutun da ke jikin bidiyon ya bayyana.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@kchrispeter ya ce:

"A zuciyar yaron cewa yake yi zan dawo gareka idan na girma."

@rosemithalexin ta ce:

"Zan dunga tuna wannan muddin rayuwata da ace nice malamar asibitin wannan kallon ba sauki."

@vik2564 ta yi martani:

"Wannan yaron fadi yake a zuciyarsa, haka za a yi, Kai zan neme ka sannan zan kashe ka na cire zuciyarka kuma na daukar maka alkawari zan yi haka."

@supersouljah2 ya kara da cewa:

"Yesu ya albarkaci wannan karamin yaron, na san guba kake kokarin saka mun Yesu na tare da ni."

Kara karanta wannan

Himma Ba Ta Ga Rago: Gurgu Ya Mayar Da Kekensa Ya Zama Shagon Siyar Da Kaya a Bidiyo

Wanke-wanke ya raba soyayya tsakanin budurwa da saurayi

A wani labari na daban, wata budurwa yar kasar Indonesiya ta datse igiyar soyayyar da ke tsakaninta da saurayinta bayan ta kai ziyara gidansu don haduwa da iyayensa.

Da isanta gidan ne dai mahaifiyar saurayin kuma mai shirin zama surukarta ta gayyace ta madafi domin tayata girki, sai dai abun bai tsaya a nan ba domin dai ta saka ta wanke-wanke bayan an gama cin abinci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel