Yan Ta'addan Zamfara Sun Sako Kwanel Din Soja Da Ƴayansa 2 Bayan Karbar N10m Kudin Fansa

Yan Ta'addan Zamfara Sun Sako Kwanel Din Soja Da Ƴayansa 2 Bayan Karbar N10m Kudin Fansa

  • Kwanel Rabiu Garba Yandoto (mai ritaya) da yaransa guda biyu da yan ta'addan Zamfara suka yi garkuwa da su sun shaki iskar yanci
  • Yandoto ya kansa ya tabbatar da cewa yan ta'addan sun sake shi bayan an biya su kudin fansa ta naira miliyan 10 ba biyar ba kamar yadda aka amince da farko
  • Tsohon sojan ya mika godiyarsa ga Allah da ya tsawaita ransa sannan ya yi godiya ga al'umma da suka taimaka wurin hada kudin fansarsa da yaransa

Jihar Zamfara - Yan fashin daji a Zamfara, a ranar Talata sun sako Kwanel Rabiu Garba Yandoto (mai ritaya) da yaransa bayan biyan naira miliyan 10 na kudin fansa.

Yayin magana da ya yi da The Punch a wayar tarho jim kadan bayan sakinsa, Yandoto ya ce an bawa yan bindigan naira miliyan 10, maimakon naira miliyan 5 da aka ambata.

Kara karanta wannan

Ke duniya: Wani matashi ya yi tsaurin ido, ya sace mahaifinsa, an ba kudin fansa N2.5m

Taswirar Zamfara
Yan Ta'addan Zamfara Sun Sako Kwanel Din Soja Da Yaransa 2 Bayan Karbar N10m Kudin Fansa. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yandoto ya ce:

"Sun karbi naira miliyan 10 kuma suka kawo ni tare da yara na kusa da garin Faskari a jihar Katsina kuma suka ce mu nemi hanyar zuwa gida.
"A halin yanzu da na ke magana da kai, bai wuce awa daya da sakin mu ba kuma mun gode Allah ba a kashe ni ba lokacin da na ke sansanin yan bindigan."

Ya gode wa dukkan wadanda suka bada gudunmawar kudi don fansarsa.

Ta yiwu sace ni na da alaka da siyasa, in ji Yandoto

Da aka tambaye shi ko sace shi na da alaka da siyasa, Yandoto ya ce:

"Akwai yiwuwar hakan. Bana son in yi magana mai yawa kan batun a yanzu."

Yan bindiga sun sace Yandoto da yaransa biyu ne kwanaki kadan da suka wuce a hanyar Gusau zuwa Tsafe lokacin da ya ke dawowa daga kauyensa.

Kara karanta wannan

An Kama Amina Guguwa Yar Shekara 50 Kan Kashe Kishiyarta Yayin Dambe A Bauchi

Daya cikin yan uwan Yandoto da ya nemi a sakaya sunansa ya fada wa The Punch cewa yan bindigan sun kira shi sun nemi kudin fansa naira miliyan 50.

A cewar dan uwan na Yandoto, daga bisani an rage kudin zuwa naira miliyan 5, bayan an dade ana tattaunawa tsakanin yan bindigan da Yandoto.

Yan fashin dajo sun sako dattijuwa yar shekara 90 da suka sace a jirgin kasar Kaduna

A wani rahoto, yan ta'addan da suka sace fasinjoji a jirgin kasar Kaduna zuwa Abuja sun sako wata dattijuwa yar shekara 90 mai suna Halimatu Atta.

Mawallafin Desert Herald, Alhaji Tukur Mamu ya tabbatar da cewa Halimatu ta shaki iskar yanci tare da yarta da wasu mutum biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel