Matashi Ya Kashe Matar Ubansa Da ’Yarta Saboda Taya Mahaifiyarsa Kishi

Matashi Ya Kashe Matar Ubansa Da ’Yarta Saboda Taya Mahaifiyarsa Kishi

  • Wani matashi a jihar Kano ya aikata mummunan aikin dana-sani, ya kashe matar ubansa da ‘yarta
  • Rundunar ‘yan sandan jihar ta yi nasarar kame shi tare da titsiye shi, ya fadi gaskiyar abin da ya aikata
  • Ya zuwa yanzu dai ana ci gaba da bincike don gano tushen matsalar tare da yiwa tufkar hanci

Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi nasarar kame wani matashin da ya kashe matar ubansa; Rabi’atu mai juna biyu ‘yar shekaru 25 da diyarta; Munawwara mai shekaru takwas.

Wannan mummunan lamari ya faru ne a unguwar yankin Fadama na unguwar Rijiyar Zaki a karamar hukumar Ungogo.

An kame matashin ne mai suna Gaddafi dan shekaru 20 bayan da mahaifinsa ya zargi shi ya kashe matar da ‘yarta, lamarin da ya tada hankalin mahaifin mai suna Sagir.

Kara karanta wannan

Daga karshe, an bindige wadanda ke samowa 'yan bindigan Arewa makamai

Matashi ya kashe matar ubansa a Kano
Matashi Ya Kashe Matar Ubansa Da ’Yarta Saboda Taya Mahaifiyarsa Kishi | Hoto: Facebook/Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: UGC

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya yada bidiyon yadda lamarin ya kaya, tare da nuna matashi da kuma makamin da ya yi amfani dashi wajen aikata kisan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya faru

Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa, wannan lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na daren ranar Asabar 7 ga watan Janairun bana.

A cewar Kiyawa, mahaifin matashin ne ya kira hukumar ‘yan sanda bayan da ya dawo gida ya tarar da gawar matarsa da ‘yarsa a kwance cikin jini.

Da yake sanar da jami’an, yace yana zargin dansa da aikata kisan kasancewar matar da dan nasa ba sa jituwa.

‘Yan sanda sun dauki mataki

Cikin gaggawa, kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Mamman Dauda ya tura jami’ai tare da umartarsu da su zagaye ko’ina don tabbatar kwashe gawarwakin zuwa asibiti.

Kara karanta wannan

Matashi Ya Hallaka Amaryar Mahaifinsa Mai Juna Biyu Kuma Ya Kashe Diyarta a Kano

Bayan kai su asibiti, likita ya tabbatar sun mutu, wanda daga nan aka shiga neman inda makashin ya shiga.

An kamo matashin a wani kango a daidai lokacin da yake kokarin cika wandonsa da iska tare da barin garin gaba daya.

Matashi ya magantu kan kisan matar ubansa

Da ya sha matsan ‘yan sanda, matashin ya amsa laifinsa, inda yace ya yi amfani da kusar ‘Screw Driver’ wajen caccakawa matar a wuya da kanta.

Hakazalika, ya ce ya yi amfani da dan kwali wajen makure wuyan ‘yar tare da aike ta madakata.

Ya kuma shaida cewa, fada ne ya fara tsakaninsa da matar mahaifinsa har ta kai ga ya aikata wannan mummunan aikin.

Dalilin da yasa ya kashe matar

Da yake bayani ga kakakin rundunar ‘yan sanda, Gaddafi ya ce ya kashe matar ne saboda ta dalilinta ne mahaifinsa ya rabu da mahaifiyarsa.

Ya ce, mahaifiyarsa ta shaida masa cewa, ba za ta iya zama da mahaifinsa ba saboda sabuwar matarsa na shiga lamarinta, kuma hakan barazana ne ga zamansu.

Kara karanta wannan

‘Yan Ta’adda Sun Kuma Kai Mugun Hari, Sun Dauke Mutane da-dama a Tashar Jirgin Kasa

Da yake bayyana taya mahaifiyarsa kishi, ya ce mahaifiyarsa ta sha yin zage-zage da matar mahaifin nasa a lokuta daban-daban.

Wani matashi ya yi tsaurin ido, ya sace mahaifinsa, an ba kudin fansa N2.5m

A wani labarin kuma, wani matashi ya yi amfani da wasu abokansa, inda ya sace mahaifinsa tare da karbar kudin fansa.

'Yan sanda sun kame shi tare da titsiye shi, ya bayyana gaskiyar abin da ya faru da kuma yadda ya aikata satar ubansa.

Ana yawan samun irin wadannan munanan laifiuka da suke da alaka da ahali a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.