'Yan Sanda Sun Bindige Wasu Kasurguman da Suka Kaiwa 'Yan Bindiga Makamai Daga Taraba Zuwa Zamfara

'Yan Sanda Sun Bindige Wasu Kasurguman da Suka Kaiwa 'Yan Bindiga Makamai Daga Taraba Zuwa Zamfara

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta yi nasarar sheke wasu ‘yan harkallar makamai a jihar ta Arewa maso Yamma
  • An bayyana yadda lamarin ya faru, da kuma yadda wasu daga cikinsu suka tsere zuwa dajin da ke kusa
  • Jami’an tsaron Najeriya na ci gaba da samun nasara kan ‘yan ta’adda a yankuna daban-daban na kasar nan

Jihar Zamfara - Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara a ranar Asabar ta tarfa tare da harbe wasu da ake zargin masu harkallar makamai ne a titin Gummi zuwa Anka a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu ya bayyana cewa, an tarfa masu harkallar makaman ne a cikin wata moto Toyota Corolla dauke da muggan makamai da za su kaiwa ‘yan bindiga a maboyarsu da Zamfara.

A cewar kakakin, tsagerun sun dauko makaman ne daga jihar Taraba a Arewa maso Gabashin Najeriya, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Mutum 20 Da Cikinsu Za'a Zabi Sabon Akanta Janar, FG

Yadda aka sheke masu kaiwa 'yan bindiga makamai
'Yan Sanda Sun Bindige Wasu Kasurguman da Suka Kaiwa 'Yan Bindiga Makamai Daga Taraba Zuwa Zamfara | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru da kuma yadda aka kwato kayayyakin aikata barna

A cewar SP Shehu:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Kayayyakin da aka kwato sun hada da kwanson makamin RPG, kwanson kayayyakin fashewa, alburusai 151 na AK47, alburusan makamin harbo jirgi 200 da wasu kayayyakin surkulle.
“Wannan nasarar ta samu ne bayan samun bayanan sirri game da motsin wadanda ake zargin a cikin mota Toyota Corolla dauke haramtattun kyayyaki daga Taraba don kai wa ‘yan ta’adda a sansanoninsu da ke Zamfara.
“An yiwa biyu daga cikin wadanda ake zargin munanan raunuka yayin da wasu suka tsere cikin daji da raunukan harbin bindiga.
Wadanda ake zargin da suka samu raunuka an dauke su zuwa asibitin kwararru na Yariman Bakura da ke Gusa, daga baya kuma likita ya ayyana sun mutu.”

Hakazalika, ya ce rundunar nema ta ‘yan sanda ne ta yi nasarar gano kayayyakin da aka ambata a sama, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

‘Yan Ta’adda Sun Kuma Kai Mugun Hari, Sun Dauke Mutane da-dama a Tashar Jirgin Kasa

Bugu da kari, an tura gamayyar ‘yan banga da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da tsaro a yankin da kuma kamo sauran wadanda ake zargin sun tsere.

An hallaka sufetan dan sanda, an sheke ‘yan bindiga a Nasarawa

A wani labarin kuma, ‘yan sanda sun yi nasarar sheke wasu ‘yan bindiga a yankin Akwanga da ke jihar Nasarawa a Arewacin Najeriya.

Rundunar ta kuma bayyana cewa, an hallaka wani jami’in dan sanda a yayin musayar wutar da aka yi da ‘yan ta’addan.

An tattara gawarwakin ‘yan ta’addan zuwa ofishin ‘yan sanda yayin da aka dauki gawar jami’in zuwa asibiti a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel