Ina Hawa Kujerar Buhari Zan Janye Tallafin Mai, Inji Dan Takarar Shugaban Kasa Peter Obi

Ina Hawa Kujerar Buhari Zan Janye Tallafin Mai, Inji Dan Takarar Shugaban Kasa Peter Obi

  • Dan takarar shugaban kasa a Najeriya ya bayyana aniyarsa ta janye tallafin man fetur idan ya zama shugaban kasa a bana
  • Peter Obi ya ce ba daidai bane yadda gwamnati ke sanya tallafin man fetur sakaka ba tare da la’akari da wasu abubuwa ba
  • Ba wannan ne karon farko da Obi ke gano lam’a a tafiyar da gwamnatin kasar nan ba, ya sha fadin hakan a baya

Najeriya - Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi ya sake jaddada cewa, zai cire tallafin man fetur idan ya zama shugaban kasa a zaben watan gobe.

Ya ce cire tallafin mai na daya daga cikin abubuwan da zai fara yi idan ya samu damar gaje kujerar Buhari a zaben mai zuwa nan kusa, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon shugaban Najeriya ya tattara dansa sun fece Turai saboda gudun rikicin zabe

A cewar Obi, tallafin mai da ake sanyawa ba komai bane face shiryayyen ta’addanci da wasu tsiraru suka tsara, kuma zai dakile hakan da zarar ya hau mulkin kasar.

Peter Obi zai janye tallafin man fetur
Ina Hawa Kujerar Buhari Zan Janye Tallafin Mai, Inji Dan Takarar Shugaban Kasa Peter Obi | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Obi ya ba da wannan tabbaci ne yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels ya shirya a ranar Lahadi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tabbas zan cire tallafin mai, inji Obi

Ya nanata cewa, zai cire tallafin tare da tabbatar da cewa, mahandama a fannin sun ci taliyar karshe har abada a kudin mai.

A cewarsa:

“Zan iya tabbatar muku zan cire shi (tallfi) nan take. Tallafi ba. Na fada a baya, shiryayyen ta’addanci ne kuma ba zan bari ci gaba da faruwa ba kuma.
“Abin da suke fada muku ba shi bane gaskiyar abin. Rabin abin da aka ambata ba tallafi bane. Na farko dai shine muna amfani da mai fiye da yadda ya kamata mu yi amfani dashi anan.

Kara karanta wannan

Fitaccen Dan Takarar Shugaban Kasa Yace Zai Ji Tsoron Allah Idan aka Zabe Shi a 2023

“Daidai muke da Pakistan a yawan jama’a. Suna amfani da kasa da kaso 50% na abin da muke amfani dashi.
“Don haka, rabin farkon, zan cire shi kuma zan ba wadanda ke shanye shi ruwa, saboda abin da ya kamata suke sha kenan, saboda mu rage kashe kudi.”

Peter Obi dai shine dan takarar shugaban kasan da ke ci gaba da nanata manufarsa ta tabbatar da rage kashe-kashen kudade a Najeriya.

Ya sha yin tsokaci tare da sukar gwamnatocin kasar nan da zuba kudade a wuraren da basu cancanta ba.

Ba wannan ne karon farko da Obi yace zai janye tallafin mai ba a Najeriya, ya sha fadin hakan a bayan tun farkon tsayawarsa ta takara, rahoton Vanguard.

Ba ruwan Zakzaky da Peter Obi

A bangare guda, Malamin 'yan Shi'a a Najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky ya karyata cewa yana marawa Peter Obi baya a zaben bana.

Kara karanta wannan

Manyan Dalilai Uku da Zasu Ja Hankalin 'Yan Arewa Su Zabi APC a 2023, Gwamna

Ya bayyana hakan ne ta bakin daya daga cikin lauyoyinsa, inda yace ba zai bayyana wanda yake goyon baya ba.

An yada cewa, Malam Zakzaky da dalibansa za su yi Peter Obi a zaben mai zuwa, amma gaskiya ta fito daga bakin malamin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel