Shugaban ’Yan Shi’a, Zakzaky Ya Bayyana Matsayarsa Game da Jita-Jitan Yana Goyon Bayan Peter Obi

Shugaban ’Yan Shi’a, Zakzaky Ya Bayyana Matsayarsa Game da Jita-Jitan Yana Goyon Bayan Peter Obi

  • Shugaban ‘yan Shi’a a Najeriya ya bayyana dalla-dalla cewa ba ya goyon bayan Peter Obi a zaben 2023 mai zuwa
  • Ibrahim Zakzaky ya bayyana hakan ne ta hannun wani lauyansa, inda ya bayyana matsayarsa game da zaben 2023
  • A bangare guda, IBB ya ce bai bayyana mara baya ga dan takarar shugaban kasan na jam’iyyar Labour ba

Najeriya - Shugaban ‘yan Shi’a a Najeriya, Ibrahim Zakzaky ya yi watsi da rahotannin da ke ikrarin yana goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi a zaben bana, Tribune Online ta ruwaito.

A baya an yada wani rahoton da ke bayyana cewa, shugaban na ‘yan Shi’a ya bi sahun tsohon shugaban kasa Obasanjo da kuma shugaban Neja Delta Edwin Clark wajen marawa Obi baya.

Kara karanta wannan

2023: Malamin addini ya yi magana kan waye magajin Buhari, yadda ya yi da ubangijinsa

Hakazalika, rahoton da ya yadu a kafafen sada zumunta ya yi kira ga ‘yan Shi’a miliyan takwas da su tabbatar da mallakar katin zabe, kuma su zabi Peter Obi a zaben shugaban kasa.

Zakzaky ya bayyana matsayarsa kan wanda 'yan shi'a za su zaba a zaben 2023
Shugaban ’Yan Shi’a, Zakzaky Ya Bayyana Matsayarsa Game da Jita-Jitan Yana Goyon Bayan Peter Obi | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Martanin Zakzaky ga rahotannin

Sai dai, daya daga cikin lauyoyin malamin, Marshall Abubakar na Falana & Falana Chambers, ya ce wannan labarin na karya ne, don haka Zakzaky bayyana marawa Obi baya ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

“Wancan labarin karya ne. Zan iya tabbatar muku cewa babu wani abu mai kama da wannan.
“Duk da cewa wasu ‘yan takarar shugaban kasa sun gana dashi, ya nisanci marawa daya daga cikinsu baya saboda ya yi imani zaben 2023 na shugaban kasa batu ne da ke da alaka da fahimta."

A kafafen sada zumunta, Obi ya samu karbuwa a idon matasa a sassan kasar nan, amma a kan samu maganganun karya game da goyon bayansa a Najeriya.

Kara karanta wannan

2023: Shugaban PDP Na Kasa Ya Lallaba Ya Gana da Gwamna Wike? Gaskiya Ta Bayyana

IBB ya musanta marawa Obi baya a zaben 2023

A makon da ya gabata ne tsohon shugaban Najeriya na mulkin Soja, Ibrahim Badamasi Babangida ya musanta labarin da ake yadawa cewa yana goyon bayan Peter Obi a zaben 2023 mai zuwa.

IBB ya bayyana cewa, sam bai san da batun ba, ya kuma ce bai zabi dan takarar da yake so ya gaji Buhari ba a zaben 2023.

Mabiya Peter Obi sanannu wajen yin babatu a kafafen sada zumunta; sukan yada maganganun na karya kan dan takarar nasu na jam’iyyar Labour.

Asali: Legit.ng

Online view pixel