Tsohon Shugaban Kasa IBB Ya Fadi Matsayarsa Kan Goyon Bayan Peter Obi a Zaben 2023

Tsohon Shugaban Kasa IBB Ya Fadi Matsayarsa Kan Goyon Bayan Peter Obi a Zaben 2023

  • Uban kasa kuma tsohon shugaban kasa, Ibrahim Badamasi Babangida ya ce bai da alaka da Peter Obi
  • Ya ce duk rubutun da ake yadawa a Twitter cewa ya goyi bayan Peter Obi ba gaskiya bane ko kadan
  • Ana ci gaba da kai ruwa rana tun bayan da tsohon shugaban kasa Obasanjo yace yana goyon bayan Peter Obi

Jihar Neja - Jigo kuma dattijon kasa, Ibrahim Badamasi Bababngida ya karyata jita-jitan da ake yadawa cewa, ya yi mubaya’a ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi a zaben bana, Tribune Online ta ruwaito.

A wata sanarwar da asusun karya na IBB @General_Ibbro ya yada a Twitter, an ambato cewa, IBB ya bayyana goyon baya ga dan takarar shugaban kasa na Labour, Peter Obi.

Rubutun na Twitter ya yi tsokaci ne ga batun Obasanjo da ya bayyana goyon baya ga Obi, inda aka ce IBB ya ce yana martana shawarin Obasanjo da kuma abin da ya yanke.

Kara karanta wannan

An Fallasa Sunan Dan Takarar Shugaban Kasan Da Tinubu Zai Amfani Da Shi Ya Lashe Zaben 2023

IBB ya karyata labarin cewa ya goyi bayan Peter Obi
Tsohon Shugaban Kasa IBB Ya Fadi Matsayarsa Kan Goyon Bayan Peter Obi a Zaben 2023 | Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Ba gaskiya bane, bana goyon bayan Peter Obi

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun IBB, Prince Kassim Afegbua ya karyata rubutun na Twitter tare da cewa, uban gidan ba ya da wani asusu a kafar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

“Ba gaskiya bane don Allah. Ku nisanci rahoton wani batun goyon baya. IBB ba shi da asusun Twitter.
“Idan zai yi magana, zai yi ne ta hanyar sanarwa mai dauke da sa hannu, ba wai a Twitter ba. Wadanda ke amfani da wancan shafin na Twitter makaryata ne.”

A tun farko ana ta kai ruwa rana tsakanin ‘yan siyasar kasar nan tun bayan da Obasanjo ya ce yana goyon bayan takarar Peter Obi, Pulse ta tattaro.

Jam’iyyar APC da ma fadar shugaba Buhari sun caccaki Obasanjo tare da dasa alamar tambaya kan kwarewarsa a siyasa

Kara karanta wannan

Matasa Yan Kishin Kasa Sunyi Gargadi Mai Karfi Ga Obasanjo Kan Goyon Bayan Peter Obi

Obasanjo ba sa'an Tinubu, Buhari da dukkan 'yan APC bane a mutunci, jigon siyasa

A wani labarin kuma, wani jigon siyasa ya ce, Obasanjo ya fi Tinubu da Buhari alheri da ma komai idan ana maganar kwatantawa.

Hakazalika, ya ce idan za a yiwa dukkan shugabannin APC kudin goro, ba za su kamo karamar yatsar Obasanjo ba.

Ya bayyana hakan ne a wani martani ga yadda APC da fadar shugaban kasa ta caccaki tsohon shugaban kasa a makon nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel