Borno: Mayakan Boko Haram Sun Halaka ‘Yan ISWAP 35 a Sabon Farmaki

Borno: Mayakan Boko Haram Sun Halaka ‘Yan ISWAP 35 a Sabon Farmaki

  • Mayakan ta’addanci na Boko Haram sun halaka mayakan ta’addanci na ISWAP 35 a wani bari da suka kai sansanonins mu da ke yankin tafkin Chadi
  • An gano cewa, mayakan Boko Haram din sun tasarwa karar da na ISWAP inda suke kai musu hari har sansanoninsu tare da kwashe makamansu
  • Majiyoyi sun sanar da yadda mayakan ISWAP suka yanke hukuncin kai farmaki yankunan tafkin Chadi da dajin Sambisa don ramuwar gayya

Borno - Mayakan ISWAP 35 ne suka rasa rayukansu a hannun mayakan ta’addanci na Boko Haram a mummunar arangama da aka yi tsakanin kungiyoyin ta’addancin.

A wata zantawa da jaridar Punch a Maiduguri a ranar Lahadi 8 ga Janairun 2023, wata majiya mai karfi tace an yi mummunar arangamar ne a ranar Asabar.

Ya cigaba da cewa, arangamar ta biyo bayan jerin hare-hare da mayakan Boko Haram suka kai karkashin jagorancin kwamandojinsu biyar, mafi shahara Abu Umaimah, kan maboyar ISWAP din.

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: 'Yan Bindiga Sun Yi Yunkurin Sace Shugaban Majalisar Dokoki a Jihar Arewa

A hare-harem wanda aka fara a tsibirin yankin Chadi da ke Toumbun Gini, Boko Haram sun kwace makamai masu yawa na mayakan ISWAP yayin da suka fatattake su daga maboyarsa.

Boko Haram a makonnin baya-bayan nan sun kai miyagun farmaki kan sansanonin ISWAP da ke dajin Sambisa da yankin Tafkin Chadi, lamarin da ya tirsasa su fito da tsarikan kare kansu daga Boko Haram.

Wata majiya mai Karfi tace farmakin da Boko Haram ke ta kai wa ISWAP yasa shugabanninsu suka yi taro a Tumbun Murhu domin tatfaunawa kan rashin iya kai farmakin kungiyar a lokutan karshen shekarar nan Kamar yadda suka tsara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rashin yin hakan Kamar yadda majiyoyi suka ce ya samo asali ne da farmakin Boko Haram kan sansanoninsu.

Majiyoyin sun kara da cewa:

“ISWAP yanzu ta yanke hukuncin kai wa Boko Haram hare-hare a manyan sansoninsu da ke tafkin Chadi da dajin Sambisa.”

Kara karanta wannan

Kano: Gaskiyar Abinda Ya Kawo Rigima Yayin Sallar Jumu'a a Masallacin Marigayi Sheikh Ahmad BUK

Sai dai, ba a samu tsokaci daga wurin kwamandan Operation Hadin Kai ba kan lamarin saboda maye gurbinsa da hukumar sojin tayi a cikin kwanakin nan.

Kamar yadda Zagazola Makama ya bayyana, an tarwatsa wasu manyan sansanonin ‘yan ta’addan biyu.

Dakaru sun halaka Boko Haram 4, Sun lalata sansanoninsu a Borno

A wani labari na daban, dakarun sojin Najeriya sun halaka mayakan Boko Haram hudu a yankin Mafa da ke Borno.

Har ila yau, sojojin Najeriya sun yi nasarar tarwatsa wasu sabbin sansanonin ‘yan ta’addan har shida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel