Borno: Jami'an Tsaro Sun Halaka 'Yan Ta'adda 4, Sun Tarwatsa Sabbin Sansanoni a Mafa

Borno: Jami'an Tsaro Sun Halaka 'Yan Ta'adda 4, Sun Tarwatsa Sabbin Sansanoni a Mafa

  • Dakarun bataliya ta 195, sashi na 1 na OPHK tare da hadin guiwar jami'an tsaro farar hula a ranar 5 ga watan Disamba sun sheke 'yan boko Haram 4 a yankin Mafa da ke Borno
  • An tattaro yadda dakarun suka yi amfani da gamsassun bayanan sirri gami da yin dirar mikiya maboyar 'yan ta'addan a yankin Karkut da Kashobe
  • Haka zalika, dakarun sun yi nasarar tarwatsa sabbin sansanoni shida na 'yan ta'addan yayin da suka yi luguden wutan da ya tilasta hatsabiban ranta a na kare

Borno - Dakarun bataliya na 195, sashin na 1 na Operation Hadin Kai, tare da hadin guiwar jami'an tsaro farin farar hula, a ranar 5 ga watan Disamba, sun halaka 'yan ta'ddan Boko Haram hudu a yankin Mafa na jihar Borno.

Kara karanta wannan

Zamfara: ‘Yan Sanda Sun Sheka ‘Dan Bindiga, Sun Kama Yaran Turji, Kachalla da Tukur

Jami'an tsaro
Borno: Jami'an Tsaro Sun Halaka 'Yan Ta'adda 4, Sun Tarwatsa Sabbin Sansanoni a Mafa. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

An tattaro yadda dakarun, suka yi amfani da wasu gamsassun bayanan sirri, gami da kai samame a maboyar 'yan ta'addan cikin yankunan Karkut da Kashobe.

Wata majiyar sirri, kwararriya wajen bada bayanai game da hare-hare da hasashe kan tsaro a tafkin Chadi ya shaidawa Zagazola Makama yadda dakarun suka yi arba da 'yan ta'addan a Karkut yayin da take bincike a Kezemari da Ladinbuta.

A cewarsa, bataliyar tare da hadin guiwar jami'an tsaron farar sun yi musayar wuta da 'yan ta'addan, yayin da tsananin luguden wutar da suka yi ya janyo raunatawa gami da halaka hudu nan take yayin da sauran suka ranta a na kare.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wasu majiyoyi sun bayyana yadda aka tarwatsa sabbin sansanoni har shida na 'yan ta'addan yayin da aka gano abubuwa masu fashewa, makamai da wayoyi a yankin.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kashe Dan Siyasa Da Wasu Mutane Uku a Wata Jahar Kudu

Kamar yadda ya bayyana, dakarun 'yan sa kai, wadanda basu kyale komai haka nan ba yayin binciken, sun bincike kafatanin yankin, tare da tarwatsa sansanin 'yan ta'adda da dama.

DSS sun cafke kwamandan ISWAP da ya farmaki Kogi ranar ziyarar Buhari

A wani labari na daban, jami'an tsaro farin kaya, DSS sun sanar da kama wani kwamandan ISWAP a jihar Kogi wanda a ke zarginsa da dasa bam a fadar basaraken kasar Ibira.

An kama shi a cikin makon nan inda ake bincike kan lamarin kafin a gurfanar da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel