Gwamna na Tuhumar Babban Basarake Kan Kin Tarbar Buhari a Ziyarar da ya kai Jihar

Gwamna na Tuhumar Babban Basarake Kan Kin Tarbar Buhari a Ziyarar da ya kai Jihar

  • Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, yana tuhumar Sarkin Ebira, Abdul Rahman Ado Ibrahim, kan kin zuwa tarar Buhari a ziyarar da ya kai jihar
  • A wasikar da gwamnan ya aike da ita, ya zargi basaraken da raini tare da rashin da'a gare shi da Shugaba Muhammadu Buhari
  • Ya bukaci rubutaccen bayani kan dalilin da zai sa ba zai dauka mataki a kansa ba cikin sa'o'i 48 da kuma bayanin baki idan ya gurfana gaban kwamiti

Kogi - Gwamnatin jihar Kogi ta na tuhumar Abdul Rahman Ado Ibrahim, Ohinoyi na kasar Ebira, kan kin zuwansa maraba da Shugaba Buhari yayin ziyarar da ya kai jihar.

Buhari ya ziyarci jihar a ranar 29 ga watan Disamban 2022 domin kaddamar da wasu kammalallun ayyuka.

A wasikar tuhumar da Enimola Eniola, daraktan al'amuran masarautu na jihar yasa hannu, yace kin zuwan basaraken wurin tarbar Buhari da gangan ne kuma hakan na iya kawo rikici a jihar Kogi da kasar Ebira.

Kara karanta wannan

Ka yi hakuri, ba zan ba da ba: Gwamnan PDP a Arewa ya hana Buhari filin kamfen

Ta kara da cewa, basaraken ya nuna raini da rashin biyayya ga ofishin gwamnan, jaridar TheCable ta rahoto.

"Takamaimai, ka san da ziyarar Shugaban kasa kuma shugaban dakarun sojin Najeriya, Ran shi ya dade, Shugaba Muhammadu Buhari zuwa Okene a ranar 29 ga watan Disamban 2022 don kaddamar da manyan ayyukan da gwamna yayi.
"A matsayin rashin mutunta jama'a da babban ofishin shugaban kasa da gwamnan, kai tsaye ka ki fitowa maraba da shugaban kasan a wurin da gwamnan jihar ya amince."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

- Wasikar tace.

“Abun ka sani ne cewa, idan babban mutum kamar shugaban kasa zai kawo ziyara ko kuma zai wuce ta jihar, Gwamna da manyan masu ofisoshin gwamnati har da sarakunan gargajiya ana tsammanin su karbe shi alamun mutunta shi da ofishin da yake."

- Wasikar ta cigaba da cewa.

Kara karanta wannan

An Fitar Da Sunayen Jihohi 10 Da Buhari Zai Halarci Kamfen Din Tinubu Da Kansa

Jaridar Leadership ta rahoto cewa, a don haka, gwamnati ta ke umarni da basaraken gargajiyan da ya miko rubutaccen bayani cikin sa'o'i 48 kan dalilin da zai sa ba za a dauka matakin ladabtarwa ba a kan shi.

Ta kara da cewa, bayanin baki zai yi amfani idan aka kafa kwamiti domin nazarin lamarin.

Buhari na dab da sauka a Kogi, bam ya tashi a fadar Ohinoyi na kasar Ebira

A wani labari na daban, bam ya tashi a kusa da fadar Sarkin Ebira sa'o'i kadan kafin saukar shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar.

Sai dai an gano cewa, wani kwamandan Boko Haram ne ya dasa bam din wanda jami'an tsaron farin kaya suka kama a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel