Dan Takarar Majalisa Na PDP A Shahararriyar Jihar Arewa Ya Rasu

Dan Takarar Majalisa Na PDP A Shahararriyar Jihar Arewa Ya Rasu

  • Dan takarar majalisar dokokin jihar Benue, Mr Mathew Akawu ya riga mu gidan gaskiya
  • Majiya daga yan uwansa ta tabbatar cewa dan takarar majalisar ya rasu a safiyar yau Juma'a bayan fama da gajeruwar rashin lafiya
  • Fom Gwottson, dan majalisa mai wakiltar mazabar Jos ta Kudu a majalisar dokokin jihar Plateau ya bayyana marigayin a matsin mutumin kirki mai kaunar mutanensa

Jihar Benue - Allah ya yi wa Mathew Akawu, dan takarar majalisar dokokin jihar Plateau a jam'iyyar PDP na mazabar Pengana ya rasu.

An gano cewa Akawu ya rasu ne a asibiti a safiyar ranar Juma'a bayan gajeruwar rashin lafiya, The Punch ta rahoto.

Taswirar Jihar Benue
Dan Takarar Majalisa Na PDP A Jihar Arewa Ya Rasu. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Dan uwan Akawu ya tabbatar da rasuwarsa

Wani majiya kusa da iyalinsa sun tabbatarwa The Punch lamarin a Jos, ranar Juma'a inda ta ce tsohon shugaban makarantar sakandaren ya rasu awanni bayan dawowa daga bikin gargajiya na karamar hukumar Bassa a jiharsa.

Kara karanta wannan

Kano: Tsabar Farin Cikin Ganin Dandazon Kanawa Yasa Tinubu Ya Kwashi Rawa Cike da Nishadi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan uwansa nasa ya ce:

"Da gaske ne cewa mun rasa dan takarar na PDP a safiyar ranar Juma'a.
"Ya tafi ya halarci bikin gargajiya na Bassa ya dawo. Amma bayan kankanin lokaci, ya kamu da rashin lafiya ya koka cewa kirjinsa na ciwo.
"An garzaya da shi asibiti kuma yau da safe ya rasu."

Akawu dattijo ne mai kaunar al'ummarsa - Gwottson

Abokinsa dan siyasa kuma dan majalisa mai wakiltar mazabar Jos ta Kudu a majalisar dokokin jihar, Fom Gwottson, ya bayyana mutuwar dan takarar na PDP a matsayin abin tada hankali.

Gwottson ya ce:

"Daga harkokin da muka yi sosai, mutum ne mai kamala da dattaku wanda ke kaunar al'ummarsa. Abin bakin ciki ne yadda muka rasa shi a yanzu. Tabbas za mu yi kewansa kuma Allah ya jikansa da rahama."

Da mutuwarsa, adadin yan takarar jam'iyyar PDP da suka rasu a jihar Plateau kafin babban zaben ya zama biyu kenan.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Shugaban BoT Ya Yi Magana Kan Yuwuwar Wasu Gwamnonin PDP Su Sauya Sheka Kafin Zabe

Innalilahi: Dan Majalisar Jihar Katsina Ya Rasu A Kasa Mai Tsarki

A wani rahoton, Dr Ibrahim Aminu Kurami, dan majalisar dokokin jihar Katinsa mai wakiltan karamar hukumar Bakari ya kwanta dama.

Ya rasu ne a Saudiyya yayin da ya tafi yin aikin Umarah kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel