Dan Takarar Gwamnan Katsina a APC Ya Karbi Daruruwam Mambobim PDP

Dan Takarar Gwamnan Katsina a APC Ya Karbi Daruruwam Mambobim PDP

  • Dan takarar gwamnan Katsina karkashin inuwar jam'iyyar APC ya karbi jiga-jigai da mambobin PDP wadan da suka sauya sheka
  • A wata sanarwa da kwamitin kamfen Dikko/Jobe ya fitar, Radda ya tallafawa yan sa kai masu yaki da rashin tsaro a Kurfi da Rimi
  • Dan takarar ya karkare zagayen kamfe a shiyyar Katsina ta tsakiya, ya dauki wasu muhimman alkawurra

Katsina - Dan takarar gwamnan Katsina a inuwar jam'iyar APC, Dakta Dikko Umaru Radda, ya karbi sabbin masu sauya sheka 1,500 daga babbar jam'iyyar Adawa PDP.

Jaridar This Day ta tattaro cewa 'yan siyasan sun koma jam'iyar APC mai mulki karkashin jagorancin tsohon Kansila a karamar hukumar Rimi, Abdul’aziz Makwalla.

Dakta Dikko Radda.
Dan Takarar Gwamnan Katsina a APC Ya Karba Daruruwam Mambobim PDP Hoto: @Drdikkoradda
Asali: Instagram

A wata sanarwa da daraktan yada labarai na kwmaitin kamfen Dikko/Jobe, Ahmed Abdulkadir, ya fitar yace Radda ya karbi masu sauya shekar ne yayin da yake karkare kamfen shiyyar Katsina a Kurfi.

Kara karanta wannan

2023: 'Dan Majalisa Dan Gani Kashenin Kwankwaso Ya Fice Daga NNPP, Ya Koma Jam'iyar Da Ya Fito

Yayin gangamin na karshe a karamar hukumar Kurfi, Radda ya ba da gudummuwar Babura 8 ga ƙungiyar Yan bijilanti.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Sanarwan, Radda ya basu tallafin ne domin taimaka masu a kokarin yaki da rashin tsaro, wanda yake da kudirin kawo karshensa idan ya zama gwamna.

Baya ga haka, Dakta Dikko ya ba da kyautar Babura 5 a karamar hukumar Rimi da kuma Babura uku da ya baiwa Yan Bijilanti a kauyen Wurma dake karkashin Kurfi.

Channels ta tattaro Wani sashin sanarwan ya ce:

"Dan takarar gwamna a inuwar APC ya jaddada aniyarsa ta yakar matsalar tsaro a Katsina idan ya zama gwamna. Ya yi alkawarin samar da aiki, inganta kiwon lafiya da habaka noma.
"Mutane da yawa daga PDP sun koma APC a kananan hukumomin, a Rimi mambobin PDP 1500 suka sauya sheka karakashin tsohon Kansila, Abdul’aziz Makwalla, haka shugabar matan PDP ta koma APC."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Takarar Majalisa 8 Na Jam'iyyar Peter Obi Sun Koma APC A Shaharariyar Jihar Arewa

APC ta karbi manyan yan takara a Jigawa

A wani labarin kuma Manyan 'Yan Takara 8 a Zaben 2023 Sun Jingine Tikitinsu, Sun Koma APC a Arewacin Najeriya

Yan takarar majalisar dokoki a inuwar Labour Party Takwas sun sauya sheka zuwa jam'iyar APC a jihar Jigawa.

Gwamna Muhammad Badaru ne ya karbe su a wani dan taro na musamman da aka shirya a gidan gwamnatin Jigawa ranar Jumu'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel