An Haramtawa Ronaldo Buga Wasansa da Aka Shirya Na Farko a Al-Nassr Bisa Dokar FA

An Haramtawa Ronaldo Buga Wasansa da Aka Shirya Na Farko a Al-Nassr Bisa Dokar FA

  • Fitaccen dan wasan kwallon kafan duniya ba zai buga wasanni har biyu ba a jere a kulob din Al-Nassr
  • Wannan ya faru ne daga kakaba masa haramcin da FA ta yi saboda saba dokar kwallon kafa
  • A watan jiya ne aka sanar da cewa, Ronaldo ya koma Al-Nassr ta kasar Saudiyya don buga wasa a can

Kasar Saudiyya - An dakatar da Christiano Ronaldo daga buga wasan farko a kulob din Al-Nassr ta kasar Saudiyya, awanni 24 kenan gabanin yadda aka tsara wasan.

Dan wasan mai shekaru 37 an shirya zai fuskanci wasa da kulob din Al-Ta’ee, kwanaki kadan bayan da Al-Nassr ta siyo shi, za ta ke bashi £173m a duk shekara.

Sai dai, a watan Nuwamba ne aka samu Ronaldo da laifin rashin da’a da cin zarafin wani a lokacin yana Manchester United kafin daga bisani ta kore shi.

Kara karanta wannan

An tabo attajirai: Waya mafi tsada a duniya ta N21.5bn ta daina daukar WhatsApp

Ronaldo ba zai buga wasan farko ba Al-Nassr
An haramtawa Ronaldo buga wasabn farko a Al-Nassr bisa dokar FA | Hoto: japantimes.com
Asali: UGC

Wannan ya faru ne bayan da ya buge wayar hannu ta wani matashi mai goyon bayan kulob din Everton a wani filin wasa, kamar yadda Evening Standard ta ruwaito.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An dakatar da Ronaldo, ba zai buga wasanni biyu ba a jere

An datakar da Ronaldo daga buga wasanni har biyu a jere, kana zai biya tarar £50,000, amma bai samu damar kammala wa’adin dakatarwar ba har aka kore shi daga United.

Jaridar Daily Mail ta ruwaito cewa, haramta masa buga wasan farko a Al-Nassr zai daura ne daga haramcin da FA ta masa na buga wasanni har biyu a jere kan wancan laifin.

A hanlin da ake ciki, Ronaldo zai yi zaman benci har na tsawon wasanni biyu; ba zai fuskanci wasa da Al-Ta’ee da Al-Shabab ba a kasar Saudiyya.

Kara karanta wannan

Daga Shigowa Shekarar 2023, Kamfonin Lantarki Sun Yi Karin Farashin Wuta a Boye

Wannan haramtawa ta buga wasa ga Ronaldo ba sabuwar aba bace, domin hakan na kunshe a cikin dokokin kwallon kafa na FA.

Zuwan Ronaldo ya jawowa kulob din Saudiyya farin jini, jama'a sun yi tururwa a Instagram

A tun farko kun ji cewa, zuwan Ronaldo Al-Nassr ya jawowa kulob din farin jini mai yawa, domin mutane sun yi dandazo don a kafar Instagram don bibiyar kulob din.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da kulob din na Saudiyya ta cire kudi ya dauko Ronaldo tare da alkawarta bashi makudan kudade.

A yanzu haka, an ce sama da mutum miliyan shida ke bibiyar Al-Nassr a Instagram, a baya basu kai miliyan 1 ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel