Wayar N21.5bn mafi tsada a duniya ta daina daukar WhatsApp

Wayar N21.5bn mafi tsada a duniya ta daina daukar WhatsApp

  • Waya mafi tsada a a duniya ta rasa manhajar WhatsApp bayan da aka yiwa zubin kwakwalwarta ingantayya
  • A cewar bayanan WhatsApp, iPhone 6 da iPhone 5 Ples na SuperNova ba za su sake daukar manhajar ba
  • Falcon, wani kamfanin kayan karau da ke birnin New York kuma ke aiki da Apple ne ya kirkiri wannan waya mai tsadar bala’i

Waya mafi tsada a duniya ta shiga jerin wayoyin da za su daina yin WhatsApp a 2023 saboda wasu gyare-gyaren zubi da kamfanin Meta ya yi.

Kamfanin Falcon da ke birnin New York ya yi shuhura wajen kera kayayyaki masu tsadar a zo a gani a duniya.

Har ila yau, su suka kirkiri wannan waya mafi tsada a duniya da kudadenta suka haura N21bn.

Waya mafi tsada ta ki daukar WhatsApp
Wayar N21.5bn mafi tsada a duniya ta daina daukar WhatsApp
Asali: Getty Images

Yaya jiki da aikin SuperNova yake?

A cewar rahotanni, kamfanin Falcon na tafiyar da kasuwancinsa ne da shugabannin kasa, fitattun mutane da ‘yan gidan sarauta a duniya.

Kara karanta wannan

Daga Shigowa Shekarar 2023, Kamfonin Lantarki Sun Yi Karin Farashin Wuta a Boye

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kuma suna kera irin kayayyakin masu tsada ne musamman ga wadannan manyan mutane a duniya domin su fita daban da sauran jama’a.

Kamfanin ya kware wajen amfani da duwatsu masu daraja da karafa masu tsada wajen kirkirar kayayyakin da ke daukar hankali fitattun mutane masu hannu da shuni.

Da yawan kayayyakin Falcon na dauke da zinare, azurfa da dai sauran kayayyakin da ake ado dasu a duniya.

Kamfanin ba shi ke kirkirar wayoyi da kansa ba, amma yakan yi aiki da Apple wajen sauya zubin halittar wayoyi don kayatar da kwastomomi.

Manyan wayoyin hannu masu tsada na kamfanin Falcon sun hada da 950 Platinum iPhone, 18k Rose Gold, da kuma 18k Yellow Gold iPhone.

Wayar da ta fi tsada na Falcon ita ce iPhone 6, kuma an yi ta da zubi biyu na yadda fadin fuskarta yake, kana an yi ta da zinare da azurfa.

Kara karanta wannan

Dandazon Masoya Sun Dira Ribas a Fatakwal Yayin Da Portable Ya Yi Waka A Tsakiyar Rafi, Bidiyon Ya Bazu

A kasan tambarin Apple da ke bayan wayar, an maka wani babban zubi na lu’u-lu’u.

Wayar na da mabambantan zubi, daidai da abin da mai saye ke bukata, haka zubin lu’u-lu’un zai kasance.

Wasu bayanai da kuma farashin SuperNova

Falcon bai bayyana takamamman nauyin lu’u-lu’un da ke jikin wayar ba, amma an yi imanin cewa, wayar ta yi tsada ne kasancewar akwai wannan dutse mai daraja a jikinta.

Hakazalika, a kanta akwai 128GB na kwakwalwar ajiya, musamman sabbin bugun da aka yi a baya-bayan nan.

Haka nan, dukkan iPhone 6 da 6 Plus na SuperNova a bude suke, za a iya amfani da su a ko’ina a duniya.

Maganar farashi, ana siyar da wayar $48.5m, kumsan N21,582,500,000.

A baya an ce, wasu wayoyi 47 ne za su daina daukar manhajar WhatsApp saboda ingantayya da aka yiwa manhajar a shekarar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel