Arewacin Najeriya Zai Zama Dubai, Ana Neman Danyen Man Fetur a Wasu Jihohi

Arewacin Najeriya Zai Zama Dubai, Ana Neman Danyen Man Fetur a Wasu Jihohi

  • Kamfanin man Najeriya watau NNPC yana ta karkata wajen gano sababbin rijiyoyin man fetur
  • Tsakanin shekarar 2020 da 2022, NNPC ya yi ta lalube ko za a iya yin dace da arzikin a Arewa
  • An binciki jihohin Sokoto, Borno, Yobe, Adamawa, Nasarawa da irinsu Neja da nufin ko za a dace

Abuja - Kamfanin NNPC na kasa yana kokarin cigaba da laluben inda za a samu arzikin danyen man fetur, hakan ya biyo bayan dacen da aka yi ne.

Wani rahoton Punch na ranar Alhamis, 5 ga watan Junairu 2023 ya nuna kamfanin man kasar ya dage wajen gano inda za a iya samun danyen mai.

Kamfanin ya ce yana aiki domin lalubo mai a yunkurin da ake yi na kara adadin arzikin man da ake hakowa da wanda za a adana saboda wata rana.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Fadi Wadanda Zai ba Mukamai da Abin da Zai Yi Kafin Kwana 100 a Aso Rock

Bayanin da NNPC ya yi yana cikin wata takarda da ta shiga hannun jaridar The Cable, dauke da nasarori da kalubalen da aka samu a yankunan.

An dage a jihohi 6

Takardar ta nuna cewa a aikin gano man da kamfanin NNPC ya yi tsakanin shekarar 2020 zuwa 2022, an fi maida hankali ne a kan jihohin da ke Arewa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jihohin Arewan da ake sa ran samun arzikin danyen mai sun hada da Neja, Nasarawa, Sokoto, Borno, Yobe, Adamawa, Bauchi sai kuma Gombe.

Man Fetur
Aikin hako mai Hoto: www.thetidenewsonline.com
Asali: UGC

Hakan ya nuna ba abin mamaki ba ne nan gaba a samu mai a yankin Arewa maso gabas, Arewa maso yamma ko dai Arewa maso tsakiyar kasar nan.

A yankin Arewa maso gabas ana sa ido a kan Borno, Yobe zuwa Adamawa, a bangaren jihohin Arewa maso tsakiya akwai Nasarawa da kuma Neja.

Kara karanta wannan

Assha: Ba a gama da jimamin Hanifa ba, wasu matasa sun sace yarinya mai shekaru 6 a Kano

Jihar Sokoto ce kurum inda ake ganin akwai yiwuwar a ci karo da danyen mai a Arewa maso yammacin Najeriya, yankin da ya ke da yawan al’umma.

Haka zalika ana tunanin yiwuwar samun arzikin a tafkin Anambra da ke kudancin Najeriya.

Ana kashe kudi sosai

Wannan lalube shi ne matakin farko da ake bi wajen hako danyen mai da gas, a nan ne ake yin binciken kasa wajen ganin ko za ayi dace da rijiyoyi.

Idan aka yi nasara, danyen man da aka saba samu a Neja Delta zai zo Arewa. Sai dai wani masani ya shaida mana aikin hako mai yana da tsada sosai.

Rijiyoyin man Kolmani

Kwanakin baya aka ji labari Shugaba Muhammad Buhari ya je kauyen Kolmani, ya kaddamar da aikin hako danyen man fetur a Arewa maso gabas.

An ji wani Lauya, Abdullahi Muhammad Tamatuwa yana yi wa Bauchi da masu ruwa da tsaki barazana zuwa kotu, ya ce Gombe ta ke da arzikin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel