Kotu Ta Yi Watsi da Karar da Ke Neman a Tsige Shugaban INEC, a Bincike Tushen Arzikinsa

Kotu Ta Yi Watsi da Karar da Ke Neman a Tsige Shugaban INEC, a Bincike Tushen Arzikinsa

  • Wani dan Najeriya ya maka shugaban hukumar zabe mai zaban kanta (INEC) a kotu kan wasu zarge-zarge
  • Ya ce yana bukatar a tsige Mahmud Yakubu daga mukamin shugaban INEC, kana a bincike silar dukiya da kadarorinsa
  • Mai shari’a ya yi duba cikin tsanaki, ya ce babu wanda zai tsige shugaban na INEC, zargin bai da makama balle tushe

Wata babbar kotun tarayya mai zamanta a Garki a babban birnin tarayya Abuja ta yi watsi da karar da aka shigar da ke neman a binciki shugaban hukumar zabe ta INEC game da zargin ba da bayanan karya kan kadarorin da ya mallaka.

A hukuncin da aka yanke a ranar Laraba, mai shari’a M.A Hassan ya gano cewa, Mahmud Yakubu na INEC ya bi ka’idojin da ake bukata wajen bayyana kadarorinsa ga hukumar gwamnati.

Kara karanta wannan

Dirama, Wani Dan Kasuwa Ya Hargitse a Kotun Musulunci Kaduna, Yace Yana Kaunar Matarsa

Mai shari’a Hassan ya kuma bayyana cewa, abubuwan da Mahmud ya mika sun yi daidai da doka, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

An yi watsi da batun tsige shugaban INEC
Kotu Ta Yi Watsi da Karar da Ke Neman a Tsige Shugaban INEC, a Bincike Tushen Arzikinsa | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Hukuncin ya kuma bayyana cewa, duba da cewa shugaban na INEC ya bi doka, don haka babu bukatar wani bincike daga hukumomin tsaro kamar yadda mai shigar da kata ya bukata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai shari’a ya yi watsi da dukkan bukatu 14 da aka nema, tare da cewa, babu mai cire shugaban na INEC daga kan kujerarsa kan wasu zarge-zarge da basu da makama balle tushe.

Yadda aka shigar da karar

Hukuncin da aka yanke yana martani ne ga kara mai lamba FCT/HC/GAR/CV/47/2022 da Somadina Uzoabaka ya shigar, Daily Trust ta ruwaito.

Uzoabaka ya yi zargin cewa, akwai lam’a da kura’kurai a kadarorin da Mahmud ya bayyanawa gwamnati, don haka ya nemi kotu ta ba hukumomin tsaro damar bincikar shugaban.

Kara karanta wannan

An Fallasa Sunan Dan Takarar Shugaban Kasan Da Tinubu Zai Amfani Da Shi Ya Lashe Zaben 2023

Har ila yau, ya nemi umarnin kotu da ta dakatar da shugaban na INEC tare da hana shi rike ofishin gwamnati a Najeriya na tsawon shekaru 10.

Martanin shugaban INEC

Da yake martani, Mahmudu Yakubu ya ce zancen Uzoabaka babatu ne marasa asali da tushe, kuma ba gaskiya bane.

Mahmud ya ba kotu takardun da suka cancanta, wadanda ke nuna tushen arzikinsa da kuma dukkan kayayyakin da ya mallaka da mai shigar da kara ke zargin na haramun ne.

Ya kuma yi ikrarin cewa, dukkan abin da ya mallaka ya samu ne ta hanyoyin da suka dace, matsayin da mai shari’a ya gamsu dashi.

Ba wannan ne karon farko da ake maka jami’an gwamnati a kotu ba kan zargin mallakar kudade ko kadarorin haramun kafin kama aiki, Buhari ma bai tsira ba, an taba maka shi a kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel