Karfin hali: Dan Najeriya ya fusata, ya maka Buhari a kotu saboda gallazawa 'yan Najeriya

Karfin hali: Dan Najeriya ya fusata, ya maka Buhari a kotu saboda gallazawa 'yan Najeriya

  • Wani lauya a Najeriya ya fusata, ya maka shugaban kasa Muhammadu Buhari a kotu saboda wasu dalilai
  • Ya bayyana cewa, shugaban kasan bai kamata ya rike mukamai biyu a lokaci guda ba, kamar yadda yake a yanzu
  • Ya kuma nuna cewa, shugaban ya gallazawa 'yan Najeriya ta hanyar haifar da tsadar man fetur a kasar nan

Jihar Legas - Festus Ogun, lauya a jihar Legas, ya shigar da karar shugaban kasa Muhammadu Buhari kan karancin man fetur da ake fama da shi a kasar nan.

A watan Fabrairu, Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA) ta tabbatar da cewa an shigo da mai mai dauke da sinadarin methanol sama da ka'idar amfanin 'yan Najeriya, TheCable ta ruwaito.

A kokarin dinke barakar, an samu tsaikon da ya haifar da dogayen layukan shan mai a gidajen mai har zuwa watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Kada haka ta sake faruwa: Shugaba Buhari ya kadu da jin labarin salwantar rayuka 100 a Imo

Lauya ya kai karar Buhari gaban kotu
Karfin hali: Dan Najeriya ya fusata, ya maka Buhari a kotu saboda gallazawa 'yan Najeriya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A cikin karar mai lamba FHC/L/CS/743/22 da aka shigar a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Legas, Ogun ya zargi shugaban kasar da haifar da “mummunar wahala, matsi da radadi” ga ‘yan Najeriya a lokacin karancin man fetur.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga cikin abubuwan da ya bijiro dasu, ya bukaci kotu ta bayyana cewa matsayin Buhari na shugaban kasa da kuma ministan man fetur ya sabawa kundin tsarin mulki.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, ya kuma yi ikirarin cewa ba a gudanar da harkokin man fetur yadda ya kamata.

Ripples Nigeria ta ruwaito shi yana cewa:

“Na kai karar shugaban kasa Muhammadu Buhari a gaban babbar kotun tarayya da ke Legas a kan irin tsananin da ‘yan Najeriya suka shiga na wahala, matsai da radadin da suka sakamakon karancin man fetur da aka fuskanta a farkon wannan shekarar."

Kara karanta wannan

Miyetti Allah: Ƴan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mambobinmu 10 Da Shanu 300, Sun Buƙaci N4m Da Bindiga Ɗaya a Anambra

Osinbajo ya yi karin-haske kan dalilin yin takara, yace akwai sirrin da shi kadai ya sani

A wani labarin, mai girma mataimakin shugaban kasa yana ganin cewa rashin adalci ne ya ki neman takarar shugaban Najeriya a zabe mai zuwa na 2023.

Daily Trust ta ce Farfesa Yemi Osinbajo ya yi wannan bayani ne a ranar Litinin, 25 ga watan Afrilu 2022 da ya kai ziyara ta musamman zuwa jihar Ondo.

Farfesa Osinbajo ya na ganin ya samu gogewar da zai rike gwamnatin Najeriya ganin yadda ya shafe shekaru har bakwai yana aiki a fadar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel