'Yan Sandan Bauchi Sun Kashe ’Yan Bindiga da Masu Garkuwa da Mutane a Wata Musayar Wuta

'Yan Sandan Bauchi Sun Kashe ’Yan Bindiga da Masu Garkuwa da Mutane a Wata Musayar Wuta

  • Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta yi nasarar hallaka wasu 'yan bindiga da ake zargin suna garkuwa da mutane
  • An kama wasu mutum da suka amsa yin garkuwa da mutum hudu tare da karbar kudaden fansa da suka kai N20m
  • A bangare guda, an kwato makamai tare da wasu kayayyakin aikata laifuka daga hannun tsagerun 'yan bindigan

Alkaleri, jihar Bauchi - An kashe wasu tsagerun da ake zargin 'yan bindiga ne da masu garkuwa da mutane a wata musayar wuta da suka da 'yan sanda da sauran jami'an tsaro a karamar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi.

An tattaro cewa, an kashe tsagerun ne a lokacin da 'yan sanda da wasu jami'an tsaro suka kai farmaki kan wata mafakar tsageru a Dajin Madam da ke zagayen gidan wasanni da kallon dabbobi na dajin Yankari.

Kara karanta wannan

2022: Wasu manyan abubuwa 10 da suka faru a 2022, sun ja hankalin jama'a a duniya

Wasu da yawa daga cikin 'yan bindigan sun tsere da raunukan harbin bindiga, kamar yaadda jaridar Punch ta ruwaito.

An sheke 'yan bindiga a jihar Bauchi
'Yan Sandan Bauchi Sun Kashe ’Yan Bindiga da Masu Garkuwa da Mutane a Wata Musayar Wuta | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wannan lamari dai ya faru ne a ranar 31 ga watan Disamban 2022, jajiberin sabuwar shekarar da muke ciki yanzu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Ahmed Wakil ya bayyana cewa, an kwato bindigogin AK-47 guda biyu daga hannun tsagerun a lokacin da suke tserewa.

An kama wasu 'yan bindiga a dajin Yankari

A bangare guda, wata rundunar 'yan sanda mai yaki da masu garkuwa da mutane ta kame wasu masu garkuwa da mutane biyu, Within Nigeria ta tattaro.

A cewar Ahmed, wadanda aka kaman sun amsa cewa, sun yi garkuwa da mutane hudu tare da boye su a dajin Yankari tare da karbar kudin fansa har N20m.

A cewar sanarwar kakakin 'yan sandan, wadanda aka kamen sun hada da Adamu Mohammed mai shekaru 33 da kuma Datti Alh Bula mai shekaru 35 kuma dukkansu 'yan unguwar Mamadi ne a gundumar Pali ta jihar.

Kara karanta wannan

Kaduna: Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Fitaccen Sarki a Arewa, Sun Tafka Ta'asa

Ya zuwa yanzu ya ce ana ci gaba da bincike don gano gaskiya tare da gurfanar dasu a gaban kuliya manta sabo.

An sheke 'yan bindiga hudu a Kaduna

A wani labarin kuma, jami'an tsaro sun yi nasarar hallaka wasu 'yan ta'adda hudu a jihar Kaduna a wani yanayi mai kama da wannan.

An kashe tsagerun 'yan bindigan ne a musayar wuta da sojoji, kamar yadda rahoto ya bayyana a jiya.

Ana ci gaba da samun nasara kan tsagerun 'yan bindiga a Najeriya, musannan ganin yadda suka addabi jama'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel