An Yi Bata Kash Da ’Yan Bindiga a Kaduna, an Hallaka ’Yan Bindiga Hudu

An Yi Bata Kash Da ’Yan Bindiga a Kaduna, an Hallaka ’Yan Bindiga Hudu

  • Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar hallaka wasu 'yan ta'addan da suka kai hare-hare wasu yankunan jihar Kaduna
  • An hallaka 'yan bindiga hudu, an kwato makamai da kudade daga hannun 'yan bindigan da aka hallaka
  • Rundunar sojin Najeriya na ci gaba da samun nasara kan 'yan bindiga a yankuna daban-daban na kasar nan

Jihar Kaduna - Rundunar Operation Forest Sanity ta hallaka wasu ‘yan ta’adda hudu tare da kwato makamai da wasu kayayyakin aikata kaifi a jihar Kaduna.

Wannan na fitowa ne daga bakin Manjo Janar Musa Danmadami, daraktan yada labarai na gidan soja a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Abuja, PM News ta ruwaito.

Danmadami ya bayyana cewa, jami’an tsaron sun dakile harin ‘yan bindiga a yankin Rafin Sarki a karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna a ranakun Lahadi da Litinin.

Kara karanta wannan

Shikenan: Daga karshe, an kashe shugaban 'yan bindigan da ya addabi mazauna jiharsu Buhari

'Yan bindiga hudu aka kashe a jihar Kaduna a makon nan
An Yi Bata Kash Da ’Yan Bindiga a Kaduna, an Hallaka ’Yan Bindiga Hudu | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yadda aka hallaka 'yan bindigan tare da kwto makamai

Ya kuma kara da cewa, an fatattakin ‘yan bindiga tare da kashe biyu da kuma kwato makami AK-47.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa, rundunar a ranar Talata ta yi kwanton bauna ga ‘yan bindiga kan wasu ‘yan bindiga a kauyen Rafin Taba, inda aka kashe ‘yan ta’adda biyu.

Ya ce jami’ai sun kwato bindigogi AK-47, alburusai, wayoyin hannu, adda, babura guda biyu da kudi N206,000.

Sanarwar ta ce:

"Babban ofishin rundunar sojoji ta yabawa dakarun Operation Forest Sanity kuma tana karfafawa jama'a gwiwa da su ba sojoji sahihan bayanan ‘yan ta’adda masu aikata laifuka.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel