'Yan Ta’adda Sun Yi Awon Gaba da Wani Hakimin Kauye da Wasu Mutane Biyu a Jhar Katsina

'Yan Ta’adda Sun Yi Awon Gaba da Wani Hakimin Kauye da Wasu Mutane Biyu a Jhar Katsina

  • Wasu 'yan bindiga sun sace wasu mutum uku a jihar Katsina; barasake, limamin gari da wani mutum na daban
  • Rahoto ya bayyana cewa, suna kan hanyar zuwa wani taron APC ne a karamar hukumar Safana sadda abin ya faru
  • Ya zuwa yanzu dai ba a samu jin ta bakin rundunar 'yan sandan Najeriya ba, musamman rundunar jihar Katsina

Safana, jihar Katsina - ‘Yan ta’adda sun sake hakimin yankin Ummadau a karamar hukumar Safana ta jihar Katsina, Barau Muhammadu tare da wasu mutum biyu da suke tare.

Su ukun, a cewar wata majiya suna kan hanyarsu ne ta zuwa hedkwatar karamar hukumar Safana domin halartar wani taron jam’iyyar APC a shirin kamfen din gwamnan jihar a ranar Laraba.

Wani mazaunin yankin, Abubakar Safana ya shaidawa jaridar Premium Times ta wayar tarho cewa, Barau Muhammadu da dan baransa da kuma wani sun gamu da ‘yan ta’addan ne mintuna kadan kafin su isa hedkwatar.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da motoci biyu suka yi karo, mutum 1 ya hallaka, yawa sun jikkata

'Yan bindiga sun sace basarake a Katsina
'Yan Ta’adda Sun Yi Awon Gaba da Wani Hakimin Kauye da Wasu Mutane Biyu a Jhar Katsina | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

‘Yan ta’addan sun garzaya dasu cikin daji, inda suka bar baburansu a inda suka sace su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

'Yan bindiga sun kira ahalin basaraken

Ya shaida cewa:

“Na yi magana da dansa (dan hakimin kenan) kuma ya shaida mani cewa ‘yan bindigan sun kira ahalin. Zan sanar daku idan na samu wani bayani.”

Ba a dai bayyana sunayen sauran mutum biyu da aka sacen ba, amma majiyar ta ce an sanar da ita limamin garin ne tare da basraaken.

Ya kuma shaida cewa Premium Times cewa, an yi watsi da hanyar Safana zuwa Ummdau tsawon shekara guda saboda yawaitar hare-haren ‘yan bindiga.

An daina bin hanyar Safana zuwa Ummadau

Ya bayyana cewa:

“Mutane suna bin zagaye ne don zuwa Safana saboda hare-haren. Bal ma, a wani lokaci an daina bin titin kwata-kwata."

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: 'Yan Bindiga Sun Bankawa Hedkwatar 'Yan Sanda Wuta

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, Gambo Isa bai dawo da sakon tes da aka tura masa don jin ta bakinsa game da wannan harin, kuma an kira wayar bata shiga.

Ina ne yankin Safana?

Safana na daya da cikin yankunan da ‘yan ta’adda suka yawaita kai hare-hare a jihar Katsina.

Yankin na da iyaka da wani kungurmin daji da ake kira Rugu da ‘yan ta’adda suka yi sansani.

Sauran yankunan da ke zagaye da Safana sun hada da Jibia, Kurfi, Batsari da Danmusa; duk suna fama da hare-haren ‘yan bindiga.

A baya 'yan bindiga sun kai hari wani yankin Katsina, inda suka hallaka wani mutum tare da tafka mummunan barna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel