Yan Bindiga Sun Banka Wuta a Hedkwatar 'Yan Sanda Ta Karamar Hukuma a Anambra

Yan Bindiga Sun Banka Wuta a Hedkwatar 'Yan Sanda Ta Karamar Hukuma a Anambra

  • Mazauna garin Ihiala, hedkwatar karamar hukumar Ihila a jihar Anambra sun shiga tsananin tashin hankali da safiyar nan
  • An ce wasu yan bindiga sun shiga garin kana suka kai hari kan babban Ofishin yan sanda na karamar hukumar
  • Rahoto ya nuna cewa maharan sun banka wa hedkwatar 'yan sanda dake garin wuta nan take yau Laraba

Anambra - Rahotannin dake shigowa sun nuna cewa yanzu haka ana cikin tashin hankali, ɗar-dar da rashin tabbas a garin Ihiala da ke ƙaramar hukumar Ihiala a jihar Anambra.

An ce mutane sun shiga wannan hali ne yayin da wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su waye ba suka farmaki hedkwatar 'yan sandan garin kuma suka banka mata wuta.

Sufetan Yan sanda na kasa, Usman Baba.
Yan Bindiga Sun Banka Wuta a Hedkwatar 'Yan Sanda Ta Karamar Hukuma a Anambra Hoto: Force HQ
Asali: Twitter

Wakilin jaridar Legit.ng Hausa a jihar Anambra, Mokwugwo Solomon, ya rahoto cewa lamarin ya faru ne a farkon awannin ranar Laraba, 28 ga watan Disamba, 2022.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Farmaki Garuruwan Kebbi, Sun Kashe Mutum Biyu Tare Da Garkuwa Da Wasu 10

Yace 'yan bindigan sun kutsa cikin hedkwatar 'yan sandan, suka bude wuta kan mai uwa da wabi don tsorata jami'an dake bakin aiki kafin daga bisani suka cinna wa ginin wuta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Har zuwa yanzu da muka haɗa muku wannan rahoton ba'a gano makasudin kai wannan hari ba. Haka nan babu sahihin bayani kan ko maharan sun kwashi makaman 'yan sanda.

Amma an tattaro cewa harin ya yi kaca-kaca da gine-ginen hedkwatar, kadarori da kuma takardun hukumar wanda ake kyautata zaton sun kai darajar miliyoyi.

Har yanzun rundunar yan sandan Anambra bata ce komai ba

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Anambra, Mista Tochikwu Ikenga, bai ɗaga kiran wayar da aka masa ko turo amsar sakonnin karta kwana da aka tura masa kan harin ba.

A halin yanzun tsohon shugaban ƙungiyar ci gaban Ihiala, Chief Okey Chikwu, ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Legit.ng Hausa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Kwana 1 da kashe tarin mutane, 'yan bindiga sun sake kai mummunan hari a Arewa

Haka zalika wani mamba a majalisar sarakunan Ihiala wanda ya nemi a sakaya bayanansa saboda tsaro ya tabbatar da kai hari hedkwatar 'yan sandan garin.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Kashe Basarake, Sun Yi awon Gaba da Wasu Uku a Jihar Neja

Alhaji Usman Garba, dagacin garin Mulo, ya rasa rayuwarsa ne a hannun yan ta'addan, waɗanda suka jefar da gawarsa suka tafi mutane uku.

A wata sanarwa da gwamnatin Neja ta fitar, gwamna Abubakar Sani Bello ya yi ta'aziyya tare da umartar dakarun tsaro su kamo maharan da suka aikata wannan ɗanyen aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel