Kai Tsaye Daga Kotu: Yadda Shari'ar AbdulJabbar Kabara Ke Gudana

Kai Tsaye Daga Kotu: Yadda Shari'ar AbdulJabbar Kabara Ke Gudana

Kotun Shari'ar Musulunci mai zama a Kofar Nasarawa ta zabi yau a matsayin ranar yanke hukunci kan shari'ar Sheikh Abduljabbar

Tun a watan Yuli na shekarar 2021, gwamnatin Kano ta gurfanar da Malamin a Kotu kan zargin maganganun ɓatanci ga Annabi SAW.

Wannan itace zama ta 30 da za'a yi tun bayan sama da shekara guda ana yi.

Kotu Ta Yankewa AbdulJabbar Kabara Hukuncin Kisa

A cewar Alkali:

Sashi na ɗati uku da sittin da uku sashin (f) ya bada hukunci haka:
Anyekewa Abduljabar hukuncin kisa Ta hanyar rataya
Saahi 380 ne ya bada wannan hukuncin ta hanyar rataya
Kuma kotu ta kwace litttafansa da ya gabatar da su a gaban kotu dan sheda
Kuma kotu ta bada umarnin kwace masallatansa gudu biyu Na filin Mushe dana Unguwar sabuwar Gwandu
Kotu ta umarci hani da saka karatunsa
Gidajen radio
Gidajen Tv
Da kafafen sadarwa
Kotu ta bashi damar daukaka kara nan da kwana 30

Lokacin hutu ya kare, Alkali ya fara rubuta hukunci

Bayan hutun kimanin mintuna ashirin da aka yi, an dawo daga hutun.

Wakilin Legit ta aiko mana da rahoton cewa:

"Shi kuma alkali ya shiga wani ofishi sannan ya fara rubuta hukunci.
Abinda kowa ke fada daga bakin yan jarida shine yadda shi Abduljabar din ya fada wa alkali maganganu.
Kuma ya nuna baya neman ko wanne irin sassauci daga wajen Alkali."

An tafi hutun rabin lokaci, sai 12:45pm za'a dawo

Bayan dakatar da Abduljabbar daga magana, an tafi hutun rabin lokaci.

An dage zaman sai zuwa karfe 12:45pm.

Wakilin Legit dake kotun yace:

"Yanzu an daga shari'ar sai daya saura kwata za'a kotu...Shari'a ce da za'a iya cewa tazo karshe tun da an riga an tabbatar da zarge-zargen da ake yiwa shi wanda gwamnati ta shiga kara kan zargi da kuma abubuwan da ake masa"

Kafin yanke hukunci, AbdulJabbar ya ce Alkali karya yake masa

Abduljabar ya fara fadawa Alkali kotun maganganu kuma yace alkali karya yake masa.

An dakatar da Abduljabar daga maganganu.

Alkali ya tabbatar da laifi kan AbdulJabbar

Mai shari'a Sarki Yola ya tabbatar da duk maganganun da Abduljabbar yake yi shi ya kirkira kuma ya jinginawa ma'aiki

Mai shari'a ya tabbatar da cewa maganganun fassara haxisan manzon Allah da Abduljabbar yace kage ne ko jingina ne, karya yake kuma hasali ma shine ya jingina kalmomin ga Ma'aiki

Mai Shari'a ya fara karanta takardun kara, kafin yanke hukunci

Online view pixel