Jaruma Rahama Sadau Ta Yi Bikin Cikarta Shekaru 29 a Duniya, Hotunan Sun Ja Hankali

Jaruma Rahama Sadau Ta Yi Bikin Cikarta Shekaru 29 a Duniya, Hotunan Sun Ja Hankali

  • A rana irin ta yau, Laraba, 7 ga watan Disamba aka haifi shahararriyar jarumar fim, Rahama Sadau
  • Rahamah ta yi murnar cikarta shekaru 29 a duniya inda ta saki hadaddun hotunanta a soshiyal midiya
  • Masu amfani da soshiyal midiya sun yi mata fatan alkhairi da addu'a yayin da wasu da dama suka mato kan haduwar da tayi

Fitacciyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Kannywood da Nollywood, Rahama Sadau, ta cika shekaru 29 a duniya, a yau Laraba, 7 ga watan Disamba.

Domin raya wannan rana, Rahama ta saki wasu zafafan hotunanta a shafinta na Instagram tana mai nuna farin ciki tsanta.

Rahama Sadau
Jaruma Rahama Sadau Ta Yi Bikin Cikarta Shekaru 29 a Duniya, Hotunan Sun Ja Hankali Hoto: rahamasadau
Asali: Instagram

Rahama ta mika godiyarta ga mahaliccinta

Jarumar ta kuma yi godiya ga Allah Ubangji da ya nuna mata wannan rana a raye kuma cikin koshin lafiya da annashuwa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Mawaki D’banj ya Shiga Hannun ICPC Kan Zargin Damfarar Miliyoyin N-Power

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Har ila yau, Rahama ta yi godiya ga Allah a kan ni’imomi da alfarmar da Ya yi mata a rayuwa.

Ta rubuta a shafinta na Instagram:

“SHAFI NA 29 ♂️
“Murna da zagayowar ranar haihuwata,
“Rahama yarinya mai kaunar kanta, karfi, kyau da ban mamaki❤️
“Akwai abubuwan godiya da dama, amma babu wanda ya fi kasancewa a raye, cikin koshin lafiya da farin ciki.
“Alhamdulillah ga wata shekara mai albarka.
“Ya Allah, Nagode da ni’imar da kayi mani ❤️♂️.”

Jama’a sun yi martani

alijita1 ya yi martani:

"Barka da zagayowar ranar haihuwa aminiya."

officialmaryambooth ta ce:

"Barka da zagayowar ranar haihuwa didi❤️."

xeesadau:

"Wannan kyau ne tsantsa na rasa mai zan ce Barka da zagayowar ranar haihuwa masoyiya."

koredebello:

"Barka da zagayowar ranar haihuwa❤️."

aycomedian:

"Barka da zagayowar ranar haihuwa ya @rahamasadau ."

Kara karanta wannan

"Ka Biyo Ni": Wata Dirarriyar Budurwa Ta Nemi Ɗan Acaba Ya Kwanta da Ita, Bidiyon Ya Girgiza Mutane

uzee_usman:

"Barka da zagayowar ranar haihuwa sarauniyar arewa ❤️."

sophiealakija

"Barka da zagayowar ranar haihuwa hadaddiyar sarauniyata "

danielamokachi:

"HBD ALLAH YA MAIMATA MA NA LAFIYA @rahamasadau ."

muh_dk8:

" nima ga karamar kyauta ta Allah yasa batayi kadanba ."

Ango da wani dan gayya sun ba hammata iska a wajen shagalin bikinsa

A wani labari na daban, mun ji cewa wani ango ya dambatu da daya daga cikin mahalarta shagalin bikinsa yayin da mutumin ya yi kokarin manna masa kudi a goshi da sunan liki.

Angon ya cire kudin tare da wurgi da shi amma sai mutumin ya koma ya dauko sannan ya yi kokarin manna masa a karo na biyu lamarin da yasa fada ya kaure a tsakaninsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel