Hukumar ICPC ta Damke Fitaccen Mawaki D’banj, Ta Garkame shi

Hukumar ICPC ta Damke Fitaccen Mawaki D’banj, Ta Garkame shi

  • Hukumar ICPC ta damke fitaccen mawakin Najeriya, Oladapo Oyebanji wanda aka fi sani da D’banj kan zarginsa da damfarar miliyoyi
  • An gano cewa, ya hada kai da wasu jami’an N-Power inda aka saka ma’aikatan bogi wadanda ake biya amma kudaden sun shigewa asusun banki mai alaka da shi
  • ICPC ta aike masa da Gayyatar amma ya ki zuwa, lamarin da yasa ta bayar da umarnin damke shi a gida ko a ketare, don haka ya mika kansa ofishinsu

Abuja - Hukumar yaki da rashawa da sauran laifuka masu alaka da ita mai zaman kanta (ICPC) ta kama tare da tsare fitaccen mawaki Oladapo Oyebanji wanda aka fi sani da D’banj, Premium Times ta tabbatar.

Mawaki D’banj
Hukumar ICPC ta Damke Fitaccen Mawaki D’banj, Ta Garkame shi. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

An kama mawakin tare da tsare shi a ranar Talata bayan jami’an ICPC sun ritsa shi, lamarin da ya tirsasa shi mika kansa ofishinsu dake Abuja, majiya da ta san kan lamarin ta tabbatar.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Kasa Ya Fadi Babban Abin da Yake Sa Jami'ai Tafka Sata a Gwamnati

Dalilin neman mawakin

Kamar yadda majiyoyin cikin gida suka ce, D’banj ya dinga wasan buya na tsawon makonni inda yake ikirarin cewa yana ketare don wasu al’amura duk don gujewa amsa gayyatarsa da aka yi kan tuhumarsa da damfara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tauraron da ya kasance hamshakin mai arziki kuma ana zarginsa da waskar da miliyoyin Naira da gwamnatin Najeriya ta ware na N-Power.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa, bincike ya nuna cewa, mawakin ya hada kai da wasu jami’an gwamnati inda aka saka ma’aikatan bogi a tsarin biyan kuma ake biyansu.

Wadannan kudin da ake biyan ma’aikatan suna shiga wasu asusun bankuna ne da aka gano suna da alaka da mawakin.

Bayan mawakin ya ki amsa gayyatar ICPC, jami’an sun ayyana kama shi a duk inda yake a Najeriya ko a waje, lamarin da yasa ya kai kansa hukumar ranar Talata.

Kara karanta wannan

Dole Ta Yi Masa? Ango Ya Yi Jugum Yana Kallon Amaryarsa Yayin da Take Girgijewa Ita Kadai A Bidiyo

Daga isar shi, an fara tuhumarsa wanda daga nan aka garkame shi. An hana belinsa saboda jami’an hukumar sun ce bai dace a yarda da shi ba saboda zai iya subucewa ya ki zuwa a yi shari’arsa.

Majiyar Premium Times tace ta yuwu ICPC ta kai shi gaban kotu ranar Laraba domin samun damar cigaba da tsare shi har sai hukumar ta kammala bincike.

Ba a samu mai magana da yawun ICPC, Azuka Ogugua ba domin jin ta bakin ta. Tana kasar waje inda take halartar wani taro.

Yan sanda sun kama hadiman Mawaki bayan mutuwar ‘dansa

A wani labari na daban, rahotanni sun bayyana cewa jami’an ‘yan sanda sun cafke dukkanin ma’aikatan gidan shahararren mawakin Najeriya, Davido kan mutuwar dansa, Ifeanyi.

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta tabbatar da cewar dukkanin ma’aikatan na tsare a hannunsu don amsa tambayoyi, Sahara Reporters ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel