Wata Mata Tace Allah Ya Sauya Mata Jinsin Jaririnta Daga Mace Zuwa Namiji, Jama’a Sun Yi Mamaki

Wata Mata Tace Allah Ya Sauya Mata Jinsin Jaririnta Daga Mace Zuwa Namiji, Jama’a Sun Yi Mamaki

  • Wata mata ‘yar Najeriya ta yi murnar haihuwar jaririnta namiji, inda ta yi ikrarin cewa, a baya binciken likita ya nuna cikin diya mace take dauke dashi
  • A cewar matar, daga daga cikin surukanta ta yi barazanar mai da ita gidansu matukar ta kuskura ta haifi diya mace
  • Matar ta ce bata kaunar samun matsala a aurenta, don haka ta godewa Allah da ya raba ta da shiga halin kunci

Wata mata ta tada kura a soshiyal midiya bayan da ya ba da labarin cewa, diyarta da aka gwada aka tabbatar mace ce a ciki ta sauya, ta haifi da namiji.

A labarin da ta yada a TikTok, matar tace a baya lokacin da take dauke da juna biyu surukarta ta yi barazanar korarta idan ta haifi diya mace.

Ta ce ta sha samun barazana daga wannan surukar ta ta, amma Allah ya masa addu’arta ya sauya lamarin.

Matar da tace diyarta ta zama namiji
Wata Mata Tace Allah Ya Sauya Mata Jinsin Jaririnta Daga Mace Zuwa Namiji, Jama’a Sun Yi Mamaki | Hoto: TikTok/@melanin_dripping0
Asali: UGC

A cewarta:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Lokacin da nake da juna biyu, ‘yar uwar mijina ta ce idan na haifi diya mace zan tafi gidan uba na daga asibiti.”

Matar ta ce wannan batu na surukarta yasa ta dage da addu’a kasancewar hoton da ta dauka na cikin a farko ya nuna tana dauke da diya mace.

A kamalansta:

“Tafiya gidanmu ba abu ne da nake so ba kuma Allah ya amsa mini. Da namiji na haifa.”

Tare da cewa dukkan ‘ya’ya a idonta daya suke kuma tana kaunarsu, ta kadu sosai. Duk da haka fa, ita surukar ‘ya’yanta mata uku ne.

Martanin jama’a a TikTok

Chizzy Lucci tace:

"Ina taya ki murna ❤ ‘yar uwa ta surukarki ba ita ce mai bayarwa ba, ki koya mata yadda za ta zama ta wadata da abin da Allah ya bata.”

user9826172725823 tace:

"Allah mai yin yadda ya so ne ina fatan Allah ya amsa addu’a ta ya bani nima nawa jaririn.”

clara bby tace:

"Ina taya ki murna ‘yar uwa Allah ba zai kunyata mu ba surukarki ta gode Allah ya ma samu mata.”

user4164655257015 tace:

"Lallai kam. Na haifi ‘ya’ya 3 maza, ni da miji na muka yanke shawarin dauko ‘ya’ya mata 3 saboda mata sun fi iya kula da ahali. Yanzu ina da ‘ya’ya maza 3 da mata 2.

prince Great yace:

"’Ya’ya kyauta ce daga Allah ka gode da duk wanda Allah ya baka ka kawai Allah ya masa albarka, amma diya mace da da namiji ai duk ‘ya’ya ne.”

Wannan ba sabon abu bane, wasu kuwa sun ma yi ikrarin sun mutu sun dawo duniya ne gaba daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel