Hukumar NAFDAC Tace Zata Sanya Kafar Wando Daya Da Wanda ke Shigo Da Man Bilicin Ba Bisa Ka'ida Ba

Hukumar NAFDAC Tace Zata Sanya Kafar Wando Daya Da Wanda ke Shigo Da Man Bilicin Ba Bisa Ka'ida Ba

  • A wani bincike da kafar labarai ta tayi, an gano Nigeria na cikinkasashen da aka fi amfani da man bilicin
  • Yan mata kan canja launin fatarsu daga baki zuwa fari dan ganin sun burge maza ko kuma abokan huldarsu
  • A wani bincike da masana lafiya sukai, sun tabbatar da yadda man bilicin ke ragewa fata karfi da kuma barazana a gareta

Abuja - Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta ce za ta kawar da kasuwanni da shaguna da masu shigo da da man bilicin wanda ba'a amince da shi ba.

Hukumar ta ce za ta fara aiwatar da aikin ne a shagunan kayan kwalliya da kuma shagunan da ake sarrafa irin mayukan wanda basu samu sahalewar hukumar ba.

Nafdac
Hukumar NAFDAC Tace Zata Sanya Kafar Wando Daya Da Wanda ke Shigo Da Man Bilicin Ba Bisa Ka'ida Ba Hoto: The Nation
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Kada Kuji Tsoron Za'ai Fari Ko Karancin Abinci, Mun Tanadi Filayen Noma - NALDA

Hukumar na bayyana wannan batun ne a wani taron bita da hukumar ta shirya, tare da hadin gwiwar kungiyar ‘yan jaridun lafiya ta Najeriya (ANHEJ).

A rahotan da jaridar The Nation ta wallafa tace mukaddashin Darakta Janar ta hukumar, Dr. Monica Eimunjeze, ta ce:

“Za mu ci gaba da aiwatar da cikakken aiki. a dan haka Muna sanar da'yan Najeriya cewa zamu fara aiwatarwa da wani aiki a shagunan kayan kwalliya saboda yawanci anan ne aka fi samun mayukan, sannan a wasu shagunan ne ake sarrafa mayukan ba bisa ka'ida ba.
"Muna sane da mayukan da ke sahalewar doka. Amma abin da muke magana akai shine waɗan da basu da waccar sahalewar. Sabida haka muke son daukar matakin akan lamarin

Akwai Masu Hada Man Bilicin A Nigeria

Mukadashin daraktan ta hukumar tace akwai wadanda ake hadawa a gida, ana amfani ne da sinadaran da da ake shigowa da su wanda hukumar ta amince musu, amma kuma sai a sarrafasu yadda bai kamata ba.

Kara karanta wannan

Tsananin yunwa: Bidiyon mata 'yan Arewa na wawar shinkafa a kan tunkuya ya tada hankali

"Yawanci sinadaran ba su da shiri ko cutarwa, amma yadda ake amfani dasu ba bisa ka'ida ba - wannan ita ce matsalar".

A yawancin lokuta, ana cakude sinadarin steroidko wasu sinadarai guda biyu ko waɗanda ma masu bilicin din basu sani ba ku sani ba., da kuma ammfani da wwasu nau'ikan ruwa wanda suma suna da barana inji ta

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel