Shugaban Sojojin Kasa, Manyan Jami’an Gwamnati 3 da Alkalai Suka daure a Kurkuku

Shugaban Sojojin Kasa, Manyan Jami’an Gwamnati 3 da Alkalai Suka daure a Kurkuku

  • An zartar da wasu hukunci a kotu da suka ba mutane mamaki daga watan Nuwamban jiya zuwa yanzu
  • Daga ciki akwai hukuncin daure Sufetan ‘Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali Baba a gidan gyaran hali
  • Bayan haka kuma an samu kotun da ta zartar da hukuncin dauri ga Shugaban hukumar EFCC ta kasa

Legit.ng Hausa ta bi, ta tattaro wadannan shari’a da aka yi a kan manyan jami’an gwamnati ko shugabannin hukumomin tsaro na kasa:

1. Shugaban EFCC (Abdulrasheed Bawa)

A wani hukunci da Chizoba Oji tayi a kotun tarayya, ta samu Abdulrasheed Bawa da laifin raina kotu bayan umarnin da aka bada a ranar 21 ga watan Nuwamba.

Oji tace shugaban na EFCC ya ki maidawa wani wanda ya shigar da kara motarsa kirar Range Rover da kuma kudi har N40m kamar yadda kotunta tayi umarni.

Kara karanta wannan

Badakalar N260m: Kotu Ta Yankewa Tsohon Shugaban Jami'ar Tarayya Ta Gusau shekaru 35 A Gidan Dan kande

Amma daga baya Alkalin tayi watsi da hukuncin da ta zartar bayan shugaban hukumar EFCC ya yi biyayya ga umarnin da aka yi na maidawa mutane dukiyoyinsu.

A dalilin haka aka fasa aika Bawa zuwa gidan gyaran hali da ke garin Kuje a birnin tarayya Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. IGP (Usman Alkali Baba)

Mai shari’a Bolaji Olajuwon na kotun babban birnin tarayya Abuja ya yankewa Shugaban ‘yan sandan Najeriya na kasa, Usman Alkali Baba, hukuncin dauri.

Shugaban Sojojin Kasa, IGP da Bawa
COAS, Shugaban EFCC da IGP Hoto: BBC, Premium Times
Asali: UGC

A hukuncin da ya zartar, Olajuwon yace Sufetan ‘yan sandan ya ki yin biyayya ga wani hukunci da kotu tayi tun a shekarar 2011, kafin ya san zai zama IGP.

Wani tsohon ‘dan sanda, Patrick Okoli ya kai kara saboda ritaya da aka yi masa a 1992. Wannan ya sa aka yankewa Usman Baba daurin watanni uku a makargama.

Kara karanta wannan

Daraktoci A Ma'aikatu rirnsu CBn da NCC Sunfi Buhari Daukar Albashi Duk Wata

3. COAS (Faruk Yahaya)

A ranar 1 ga watan Disamba, wata babban kotun jihar Neja ta samu Janar Faruk Yahaya da laifin raina mata hankali, hakan ya jawo aka yanke masa hukuncin dauri.

Alkalin da ta yanke hukunci a garin Minna, Halima Abdulmalik tace a tsare Shugaban hafsun sojojin kasan a gidan gyaran hali da yake babban birnin jihar Neja.

Baya ga shugaban hafsun sojojin kasa, an samu Manjo Janar Olugbenga Olabanji da laifin raina kotu. Kotu tana so su zauna a magarkama har sai sun wanke kan su.

Aisha Buhari a Kotu

A yau aka samu labari Hajiya Aisha Buhari Mai dakin shugaban Najeriyan tana cikin shaidu biyar da jami’an tsaro za su gabatarwa Alkali a shari'ar da ake yi a kotu.

Abin ban mamaki a cikin wadanda za su bada shaida a shari’ar da ake yi Aminu Adamu har da uwargidar shugaban Najeriya da wasu manyan jami'an 'yan sanda.

Kara karanta wannan

Ya’yan Buhari sun shiga yakin neman zaben mata na Tinubu-Shetima a Katsina

Asali: Legit.ng

Online view pixel